Tsufa Ya Yi Gardama: An Kama Tsoho Dan Shekara 60 na Safarar Bindigogi
- Rundunar 'yan sanda ta cigaba da kara kaimi wajen yaki da safarar makamai a Najeriya a kokarin yaki da 'ya ta'adda masu kai hari a yankuna
- Rahotanni sun nuna cewa an kama wani tsoho dan shekara 60 da ake zargi yana safarar makamai da ake amfani da su ba bisa ka'ida ba
- Kakakin 'yan sandan jihar Cross River, Sunday Eitokpah ya yi karin haske kan kama tsohon da matakan da hukumomi za su dauka a kansa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Cross River - ‘Yan sandan Cross River sun kama wani tsoho mai shekaru 60, Okon William da ake zargi da safarar bindigogi, a karamar hukumar Odukpani ta jihar.
Rahotanni sun nuna cewa an kama shi ne a unguwar Ubanbat bayan samun sahihan bayanan sirri daga jami’an sashen yaki da garkuwa da mutane, inda aka kwato bindigogi guda biyu da aka kera a gida.

Source: Original
An kama tsoho mai safarar makamai
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘yan sandan, ASP Sunday Eitokpah, ya fitar a X, ya ce samamen da suka yi ya kai ga cafke wanda ake zargin tare da kwato makaman da ke hannunsa.
Sanarwar 'yan sanda ta ce:
“A kokarinta na yaki da yaduwar makamai ba bisa ka’ida ba, rundunar ‘yan sandan jihar Cross River, ta kama wani da ake zargi da safarar bindigogi mai suna Okon William mai shekaru 60, tare da kwato bindigogi guda biyu da aka kera a gida a karamar hukumar Odukpani.
“Kamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da jami’an sashen yaki da garkuwa da mutane suka samu kan ayyukan wani da ake zargi da safarar makamai a unguwar Ubanbat.
“Bayan samun bayanan, jami’an ‘yan sanda sun yi gaggawar tura jami’ansu yankin inda suka kama wanda ake zargin a ranar 19 ga Afrilu, 2026 da misalin karfe 5:00 na yamma.”

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kai farmaki fada, sun yi garkuwa da mai martaba Sarki a Najeriya
Rundunar ta kuma bayyana cewa:
“Bayan kama shi, an yi masa cikakken bincike wanda ya kai ga gano bindigogi guda biyu da aka kera a gida da ya boye.”

Source: Twitter
Zargin da aka yi wa tsohon
Binciken farko ya nuna cewa ana zargin mutumin da shiga safarar makamai ba bisa ka’ida ba, kuma yana amfani da dabarun boye ayyukansa domin guje wa kama shi.
Sanarwar ta kara da cewa ya riga ya bayar da muhimman bayanai da ke taimaka wa binciken da ake yi kan kerawa da safarar makamai ba bisa ka’ida ba.
Punch ta wallafa cewa sanarwar ta kara da cewa:
“Yanzu haka wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda, kuma za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike. Ana kara kokari domin cafke sauran mambobin wannan kungiyar tare da kwato karin makamai,”
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Rashid Afegbua, ya bukaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai.
An kai hari a jihar Kwara
A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da manyan makamai sun kai hari kan sojojin Najeriya da 'yan sa-kai a jihar Kwara.
Biyo bayan harin, an sanar da cewa 'yan ta'addan sun kashe dakarun sojojin Najeriya uku da wasu 'yan banga biyu da suke taimaka musu.
Bayan kashe jami'an tsaron, an samu bayanan cewa 'yan ta'addan sun sace abubuwan hawa da suka hada da babur da harsashi da dama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

