Yunkurin Juyin Mulki: Kotu Ta Yi Umarni a Saki Shehin Darika, Khalifa Zariya
- Babbar kotun tarayya ta yi umarni da a saki Sheikh Sani Abdulkadir Zariya bayan tsare shi kan zargin yana da hannu a yankurin juyin mulki
- An tsare malamin ne a Abuja yayin da ya je hedkwatar EFCC na niyyar warware wasu matsaloli da suka shafi asusun bankin da yake aiki da shi
- Biyo bayan tsare shi, an yada rade-radin ya mutu, lamarin da ya tayar da kura tare da barin wasu daga cikin makusantan shi su ziyarce shi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin sakin Sheikh Sani Abdulkadir Zaria ba tare da sharadi ba.
A cikin hukuncin da mai shari’a Peter O. Lifu ya yanke a ranar Litinin, kotun ta ce tsare malamin na tsawon lokaci ba tare da ingantaccen umarnin kotu ba ya take hakkinsa.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa kotun ta ce an take hakkinsa na ‘yancin kai, sauraron shari’a cikin adalci da kuma ‘yancin zirga-zirga kamar yadda kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada.
Hukuncin kotu kan Khalifa Zariya
A cikin takardar hukuncin da aka tabbatar da sahihancinta, karar mai lamba FHC/ABJ/CS/55/2026 ta kasance karkashin dokokin kare hakkin dan Adam na 2009.
A karkashin bayanan da Sheikh Khalifa Zariya ya shigar da kara kan wadanda ake tuhuma guda biyar; hukumar EFCC, DIA, Antoni Janar na Tarayya, bankin Jaiz, da kuma SSS.
Umarnin sakin Khalifa Zariya
Rahoton jaridar Daily Nigerian ya nua cewa bayan zaman da ta yi, kotun ta ba da umarnin a saki mai karar nan take ba tare da wani sharadi ba.
Haka kuma ta ayyana takaita amfani da asusun bankinsa na Jaiz Bank ba tare da umarnin kotu ba a matsayin doka ba, tare da cewa an take hakkinsa.
Alkalin ya yanke hukuncin cewa EFCC da bankin Ja'iz za su biya Sheikh Khalifa Zariya Naira miliyan 1 bisa takaita aiki da asusun bankinsa ba bisa ka’ida ba, yayin da DIA da DSS za su ba shi Naira miliyan 4.
Bugu da kari, kotun ta umurci DIA da SSS da su wallafa takardar neman afuwa ga mai karar bisa tanadin sashe na 35(6) na kundin tsarin mulki.

Source: Facebook
Rahotanni sun nuna cewa kotun ta kuma umurci bankin Jaiz da ya cire takunkumin da aka sanya a asusun bankinsa nan take.
A yayin shari’ar, lauyan mai karar karkashin jagorancin Sunusi Musa ya bayyana a kotu tare da tawagarsa da suka hada da A.M. Mohammed, Bala Umar, P.A. Adewuyi da sauransu.
An daga shari'ar masarautar Kano
A wani labari, mun kawo muku cewa kotu ta yi zama game da shari'ar da ake a kan sarautar Kano da Babba Dan Agundi ya shigar da kara.
A yayin zaman kotu da aka yi, an daga sauraron shari'ar zuwa bayan zaben 2027, inda za a koma gaban alkali a watan Afrilun shekara mai zuwa.
Babban Dan Agundi ya bayyana cewa matakin da kotun ta dauka ya yi daidai, inda ya ce hakan zai ba su dama su yi nazari kan shari'ar.
Asali: Legit.ng

