Trump: "Abin da zai Faru da Iran idan ba Ta Amince da Yarjejeniyar Amurka ba"
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce dole ne Iran ta shiga tattaunawa ko ta fuskanci matsaloli da ba a taɓa ganin irinsu ba
- Ya jaddada cewa Amurka ba za ta amince Iran ta mallaki makamin nukiliya ba ko ana cikin wane irin yanayi
- Trump na wannan barazana bayan Iran ta nuna rashin yarda da Amurka da aka yi zargin ta karya yarjejeniyar da aka cimma
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
US – Shugaba Donald Trump, ya bayyana cewa yana da ƙwarin gwiwar cewa Iran za ta amince ta shiga tattaunawa da Amurka duk da ta ɗan ja ƙafa.
Donald Trump ya yi gargadin cewa idan hakan ba ta faru ba, ƙasar za ta fuskanci matsaloli masu tsanani fiye da duk abin da ta taɓa gani a baya.

Kara karanta wannan
"Ta yaudare mu sau 2," Iran ta sake tona asirin Amurka ana shirin komawa teburin sulhu

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta wallafa cewa Trump ya yi wannan bayani ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shirin rediyo na The John Fredericks Show.
Donald Trump ya magantu kan sulhu da Iran
Anadolu Ajansi ta wallafa cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ce za a cimma yarjejeniya da Iran ba tare da an samu akasin sulhu ba.
A cewarsa:
“Za su yi sulhu, kuma idan ba su yi ba, za su ga matsaloli irin wanda ba su taɓa gani ba.”
Ya ƙara da cewa yana fatan Iran za ta amince da yarjejeniyar da aka bayyana cike da adalci da za ta taimaka mata wajen farfaɗo da tattalin arzikinta.
Duk da haka, ya jaddada cewa akwai sharadi mai ƙarfi—ba za a bari Iran ta mallaki makamin nukiliya a kowane irin yanayi ba.
Gargaɗin da Trump ya yi wa Iran
Trump ya yi gargaɗi mai tsauri kan batun makaman nukiliya, yana cewa bai kamata a bari Iran ta samu damar mallakar irin wannan makami ba. Ya ce hakan na iya jawo babbar barazana ga duniya baki ɗaya.

Kara karanta wannan
Iran ta jingine batun zaman sulhu bayan Amurka ta kai wa jirginta hari, ta shirya ramuwa

Source: Facebook
A kalamansa, ya ce:
“Ba za su samu makamin nukiliya ba. Ba za su samu damar mallaka ko kusantar hakan ba. Ba za mu bari hakan ta faru ba.”
Ya ƙara da cewa irin wannan makami na iya haifar da rushewar duniya baki dayanta, don haka kasar Amurka ba za ta lamunci hakan ba.
Trump ya bayyana cewa matakan da Amurka ta ɗauka kan Iran ba wai sakamakon zaɓinta ba ne, tilas ne a dauke su.
Ya ce:
“Ba mu da wani zaɓi dangane da Iran. Ba kamar muna da damar zaɓi ba ne. Dole ne mu yi abin da muka yi.”
Dalilin Trump na fara yaƙi da Iran
A baya, mun wallafa cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi tsokaci kan batun cewa Isra'ila ce ta sanya shi ya fara yaki da jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Donald Trump ya bayyana cewa ko kadan Isra'ila ba ta lallaba shi ba domin ya fara kai hare-hare kan kasar Iran ba kamar yadda wasu a ciki da wajen Amurka ke zato.
Shugaban na Amurka ya fito ya kuma soki kafafen yada labaran kasar masu sukar yakin da ake yi da Iran a Gabas ta Tsakiya wanda aka fara a ƙarshen watan Fabarairu, 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng