Mataimakin Kakakin Majalisa Ya Gamu da Mummunan Hatsari, An Kwaso Motar da Yake Ciki
- Hatsarin mota ya rutsa da mataimakin kakakin Majalisar dokokin jihar Nasarawa, Rt. Hon. Muhammad Adamu Oyanki a titin Keffi zuwa Akwanga
- Rahotanni sun nuna cewa duk da motar da yake ciki ta yi kaca-kaca, Hon Oyanki ya tsira kuma yana cikin koshin lafiya
- Kakakin Majalisar Dokokin Nasarawa, Rt. Hon. Dr. Danladi Jatau, tare da wasu ‘yan majalisa, sun kai ziyara domin duba motar da hatsarin ya rutsa da ita
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Nasarawa - Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Rt. Hon. Muhammad Adamu Oyanki, ya tsira daga wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyar Keffi zuwa Akwanga a ranar Litinin.
Lamarin, wanda ya faru da misalin karfe 10:00 na safe, ya jefa fargaba a zukatan al’umma da ‘yan majalisa, duk da cewa babu asarar rai a hatsarin.

Source: Facebook
Mataimakin kakakin Majalisa ya yi hatsari
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa motar da ya ke ciki ta samu mummunar barna sakamakon hatsarin, inda daga bisani aka kwashe ta zuwa harabar Majalisar Dokoki da ke Lafia.
Kakakin Majalisar Dokokin Nasarawa, Rt. Hon. Dr. Danladi Jatau, tare da wasu ‘yan majalisa, sun kai ziyara domin duba motar da hatsarin ya rutsa da ita a ranar Litinin.
Da yake magana kan lamarin, Jatau ya bayyana hatsarin a matsayin abin takaici, amma ya nuna godiya ga Allah da ya ceci rayuwar mataimakinsa.
A wani sako da ya wallafa a Facebook, Jatau ya ce:
“Mun gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya kubutar da rayuwar Mataimakin Kakakin Majalisa daga wannan hatsari. Muna godiya da yake raye kuma cikin koshin lafiya."
Wane hali mataimakin shugaban majalisar ke ciki?
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa Mataimakin Kakakin, Hon. Muhammad Oyanki yana cikin yanayi mai kyau bayan hatsarin, kuma ba a samu wani mummunan rauni da zai barazana ga rayuwarsa ba.
Wannan lamari ya sake jaddada muhimmancin kiyaye dokokin hanya da kuma taka tsantsan yayin tuki, musamman a manyan hanyoyi da ake yawan zirga-zirga.
Haka kuma, ‘yan majalisa da dama sun bayyana farin cikinsu da jin cewa Oyanki ya tsira, inda suka bayyana hakan a matsayin babban abin godiya ga Allah.

Source: Facebook
Hon. Oyanki zai koma bakin aiki
Ana sa ran Mataimakin Kakakin Majalisar zai ci gaba da gudanar da ayyukansa na majalisa ba tare da wata tangarda ba, duba da cewa an tabbatar yana cikin koshin lafiya.
Lamarin ya kuma ja hankalin jama’a kan yadda hadurran mota ke ci gaba da zama barazana ga rayuka da dukiyoyi, musamman a manyan hanyoyin Najeriya, inda ake bukatar karin wayar da kai da tsaurara matakan tsaro.
Tsohon dan majalisa ya yi hatsari
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan Majalisar wakilai, Hon. Ogbonna Nwuke, ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a jihar Ribas.
Lamarin ya faru ne a kan titin Eastern By-pass, kusa da Hypercity a cikin birnin Fatakwal yayin da Hon. Nwuke ke tuƙa motar da kansa.
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin ga manema labarai, Nwuke ya ce ya gode wa Allah bisa yadda ya tseratar da shi daga hatsarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

