"Mun ba Ku Awanni 72": Boko Haram Ta Yi wa Gwamnati Rashin Kunya bayan Sace Mutum 416 a Borno

"Mun ba Ku Awanni 72": Boko Haram Ta Yi wa Gwamnati Rashin Kunya bayan Sace Mutum 416 a Borno

  • Ƙungiyar Boko Haram ta bayar da wa’adin sa’o’i 72 tare da barazana kan mutane 416 da ta yi garkuwa da su a wani daji
  • 'Yan ta'addan sun yi barazanar rarraba su zuwa wurare daban-daban idan ba a biya bukatunta da ta zayyana wa gwamnati ba
  • Boko Haram ta yi wa gwamnati taƙama, inda ta ƙalubalance ta a aiko dakaru sun zo su kwaci mutanen idan an isa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno –Ƙungiyar ƴan ta'addan Boko Haram ta fitar da wani bidiyo inda ta ƙalubalanci gwamnatin Najeriya kan yunƙurin ceto mutane 416 da aka sace a jihar Borno.

A cikin saƙon, ƙungiyar ta bayyana cewa idan ba a biya bukatunta ba cikin sa’o’i 72, za ta kai waɗannan mutane wurare daban-daban da ka iya sa a daina ganin su har abada.

Kara karanta wannan

ADC ta gano barazana a dawo da ƴan ta'adda cikin jama'a, ta gargaɗi gwamnatin Tinubu

'Yan Boko Haram sun fitar da bidiyo
Taswirar jihar Borno inda aka sace mutane sama da 400 Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Punch ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa an samu bidiyon ne da sanyin safiyar Litinin, 20 ga watan Afrilu na shekarar 2026.

Kungiyar Boko Haram ta fitar da bidiyo

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa mayaƙan, sanye da kayan soji, sun bayyana cewa suna shirye don tunkarar duk wani hari idan gwamnati ta zaɓi amfani da ƙarfi maimakon biyan bukatunsu.

Sun kuma ce suna maraba da duk wani yunƙurin ceto mutanen da ƙarfin soji idan har gwamnati na ganin wannan ce hanya mai ɓulle wa.

Saƙon da aka yi da harshen Hausa, tare da fassara zuwa Turanci, ya nuna cewa ƙungiyar ta kira kanta da Jama’atu Ahlis-Sunna Lidda’awati Wal-Jihad ƙarƙashin wani jagora da suka ambata.

Sun jaddada cewa wannan shi ne saƙonsu na farko kuma na ƙarshe ga gwamnati da kuma wata ƙungiya ta matasa a yankin Borno ta Kudu.

Boko Haram ta ƙalubalanci gwamnati

Kara karanta wannan

Jigon APC: "Ba aikin Tinubu ba ne zai sa mu ci zaɓen 2027"

A cewar maharan, idan lokaci ya cika ba tare da an biya bukatunsu ba, za su kwashe duk waɗanda ke hannunsu, daga ciki har da mata da yara, zuwa wurare daban-daban.

Boko Haram ta ƙalubalanci gwamnatin Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Sun kuma gargadi masu ruwa da tsaki da kada su wuce wa’adin da suka bayar. Duk da haka, bidiyon bai bayyana takamaiman bukatun da suke nema ba.

A gefe guda, an ruwaito cewa ƙungiyar ta buƙaci N5bn a matsayin kudin fansa domin sakin mutanen da Boko Haram ta yi garkuwa da su.

Shugaban ƙungiyar matasan Borno ta Kudu, Samaila Kaigama, ya tabbatar da hakan, yana mai cewa an isar da buƙatar ta hanyar bidiyo wanda aka bayyana a matsayin gargadi na ƙarshe.

Ya bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin sasanci tsakanin masu ruwa da tsaki domin ganin an kubutar da matan da yara 416 da aka sace daga Ngoshe.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da sauran ‘yan Najeriya masu hali da su gaggauta shiga tsakani ta hanyar da ta dace domin ceton rayukan waɗannan mutane.

An gyara halin tubabbun ƴan Boko Haram

A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin tarayya ta kammala shirin sauya tunani da gyaran halin tsofaffin 'yan ta'adda 744 da suka fito daga jihohi daban-daban da wasu kasashe.

Kara karanta wannan

Gabanin 2027, ADC ta fada wa Tinubu maganar da za ta jefa masa tsoron 'yan adawa

Mafi yawan tsofaffin 'ya ta'addan sun fito daga jihar Borno da ke fama da matsalar Boko Haram da wasu jihohi kamar Kano, Yobe da sauransu, inda aka gyara masu tunani.

Shugaban gwamnoni Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya kira ga tsofaffin 'yan ta'addan da su yi amfani da damar da suka zamu wajen zamowa mutanen kirki a al'umma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng