Bidiyo: Tsofaffin Ƴan Sanda Sun Rufe Ƙofar Shiga Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya
- Ƴan sandan Najeriya da suka yi ritaya sun gudanar da zanga-zanga a Abuja domin neman a fitar da su daga tsarin fansho na bai-ɗaya (CPS)
- Masu zanga-zangar sun buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa dokar ficewa daga tsarin fansho hannu wadda majalisar ƙasa ta amince da ita
- Tsofaffin jami'an sun koka kan yadda suke mutuwa cikin yunwa da talauci sakamakon ƙarancin kuɗaɗen da ake ba su bayan shekaru 35 na aiki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Tsoffin jami’an ƴan sandan Najeriya da iyalansu, ƙarƙashin ƙungiyar PROFN sun gudanar da zanga-zanga a yau Litinin, 20 ga Afrilu, 2026, inda suka toshe ɗaya daga cikin ƙofofin shiga fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Masu zanga-zangar sun fito ne domin nuna rashin amincewarsu da tsarin fansho na gudunmawar ma'aikata (CPS).

Source: Twitter
Tsofaffin 'yan sanda sun yi zanga-zanga
Sun ɗauki alluna masu dauke da rubuce-rubucen neman adalci, inda suke tambayar dalilin da ya sa aka fitar da sojoji da jami’an DSS daga tsarin fanshon PenCom, amma aka bar ƴan sanda a ciki, in ji rahoton Punch.
Rahoton ya nuna cewa masu zanga zangar dai sun kasance suna rera waƙoƙin nuna cewa "ƴan sanda na aiki, amma PenCom na cinye musu kuɗi.
Babban dalilin wannan zanga-zangar shi ne matsa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu lamba domin ya sanya wa dokar fitar da ƴan sanda daga tsarin fanshon hannu.
Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta riga ta amince da wannan dokar tun ranar 4 ga Disamba, 2025, kuma aka aika wa fadar shugaban ƙasa takardun a ranar 16 ga Maris, 2026.
Bukatar tsofaffin 'yan sanda ga Tinubu
A cewar tsofaffin jami'an, wannan dokar idan ta zama doka za ta cece su daga abin da suka kira "tsarin bauta da ke kashe mutane kafin lokacinsu."

Kara karanta wannan
Alkawuran da Tinubu, Atiku da wasu da ke neman takarar shugaban kasa suka fara yi wa talakawa
Suna ganin cewa matuƙar aka fitar da su daga wannan tsari, za su iya samun haƙƙoƙinsu yadda ya kamata domin kula da iyalansu da kuma gina gidajen kansu.
Wani tsohon mataimakin babban jami’in ƴan sanda (ASP), Nurudeen Dahiru, ya yi magana cikin fushi, inda ya ce ba roƙo suka zo yi ba, face fafutukar neman haƙƙinsu bayan sun bauta wa ƙasa tsawon shekaru 35.
Ya ce yawancinsu ba su da abincin da za su ci, kuma ba su iya tura ƴaƴansu makaranta saboda tsananin talauci.

Source: Getty Images
"N24,000 ake ba mu," tsohon sifeta
Haka kuma, wani jami’in da ya yi ritaya a matsayin Sifeta ya koka da cewa N24,000 kacal ake ba shi a wata, adadin da ya ce ba zai iya yin komai da shi ba a halin yanzu.
Masu zanga-zangar sun lashi takobin cewa ba za su ja da baya ba har sai an biya musu buƙatunsu, domin a cewarsu, "an kusa kure su" kuma "gwamma mutuwa da wannan irin rayuwa."
Kalli bidiyon zanga zangar a nan kasa:
Kisan bawan Allah ta jawo zanga-zanga
Kwanakin baya ne aka samu labarin yadda aka kashe wani bawan Allah bayan sallar Asuba a masallaci a yankin Ogo-Oluwa a birnin Osogbo a Osun.
'Yan sanda sun kai dauki, sun kama babban limamin masallacin da wasu mutum uku a garin na Osun da ke cikin yankin Kudu maso yammacin Najeriya.
A sakamakon haka, 'yan uwan mamacin sun barke da zanga-zanga, sun hana sallar Juma'a a masallacin domin ganin sun dauji fansar jinin marigayin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

