Bayan Sauya Shekar Kwankwaso, Wasu Manyan Jiga Jigan Siyasar Najeriya Za Su Koma ADC

Bayan Sauya Shekar Kwankwaso, Wasu Manyan Jiga Jigan Siyasar Najeriya Za Su Koma ADC

  • Jam'iyyar ADC ta ce nan ba da jimawa ba za ta karbi wasu manyan 'yan siyasar Najeriya a shirye-shiryen tunkarar zaben 2027
  • Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya ce bayan Rabiu Kwankwaso, jam'iyyar za ta kara jawo manyan jiga-jigai
  • Ya soki APC da hukumar zabe, INEC kan rikicin cikin gida da ADC ke fuskanta, yana mai cewa hakan ya kara masu kwarin gwiwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar ADC ta ce haɗakar ‘yan adawa na ci gaba da faɗaɗa yayin da ake sa ran karin manyan ‘yan siyasa za su shiga cikinta kafin babban zaben 2027.

Wannan na zuwa ne bayan shigar tsohon dan takarar shugaban kasa, kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, cikin haɗakar ADC.

Jam'iyyar ADC.
Peter Obi, Atiku Abubakar da wasu manyan jiga-jigan hadaka a taron ADC a Abuja Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi a gidan talabijin na Channels yau Litinin.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ADC ta yi maganar hadewa da PRP, ta bayyana shirin da take yi

Jam'iyyar ADC na kara karbuwa

Bolaji Abdullahi ya ce tun farko sun tsara bin hanyoyin da suka dace don haɗakar ta ci gaba da girma, yana mai cewa ana sa ran karin manyan jiga-jigan siyasa za su biyo baya.

"Hadakar mu tana ƙara girma. Tun daga farko mun yi hasashen cewa za ta bunƙasa. A farko kwankwaso ba ya tare da mu, amma yanzu ya shigo cikinmu.
"Muna sa ran cewa a cikin kwanaki masu zuwa, ƙarin mutane, manyan jiga-jigai a siyasar Najeriya, za su shigo," in ji shi.

Manyan ‘yan siyasa sun haɗu a ADC

Ya bayyana cewa wasu fitattun ‘yan siyasa kamar Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi, Aminu Tambuwal da Nasir El-Rufai sun riga sun haɗu a ADC domin fuskantar zaɓen 2027

"Manufar su da mu gaba daya, ita ce haɗa ƙarfi a wuri guda domin kayar da jam’iyyar APC mai mulki da Shugaba Bola Tinubu," in ji shi.

Kara karanta wannan

Batun takarar Kwankwaso da Obi na kara karfi, an kafa sabuwar kungiya

INEC da rikice-rikicen jam’iyya

Bolaji Abdullahi ya zargi jam’iyyar APC da haddasa rikice-rikicen da ke addabar jam’iyyun adawa

Duk da haka, ya ce matsalolin cikin gida da kuma matakin da hukumar INEC ta ɗauka na rashin amincewa da shugabancin jam’iyyar ya kara wa hadakar karfi a sassan kasar nan.

Bolaji Abdullahi.
Mai magana da yawun jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: Bolaji Abdullahi
Source: Twitter

Kakakin ADC na kasa ya jaddada cewa hanya mafi dacewa ta kawo sauyi a siyasar Najeriya ita ce haɗin kan dukkan ‘yan adawa a ƙarƙashin inuwa guda.

Abdullahi ya bayyana cewa jam’iyyar ADC na kan hanya madaidaiciya wajen cimma burinta na kawo sauyi a ƙasar nan, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

ADC ta musanta jita-jitar hadewa da PRP

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta hadakar yan adawa a Najeriya ta bayyana cewa ba ta tunanin hadewa da jam'iyyar PRP kamar yada mutane ke yadawa.

An yi ta samun rade-radin cewa shugabannin adawa na iya neman haɗewa da wasu jam’iyyun siyasa, ciki har da PRP, gabanin babban zaɓen 2027.

Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi ya bayyana iƙirarin a matsayin ƙarya, inda ya nuna cewa shugabancin haɗakar jam’iyyun ba sa cikin wata tattaunawa da wata jam’iyyar siyasa a halin yanzu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262