Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Kashe Sojojin Najeriya, Sun Tafi da Motar Yaƙi
- Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun kashe aƙalla sojoji uku da ƴan banga biyu a wani hari da suka kai garin Kemanji da ke ƙaramar hukumar Kaiama
- Maharan sun yi awon gaba da motar yaƙi ta sojoji, makamai, harsashi, da kuma babura har guda 12 bayan sun mamaye sansanin jami'an tsaron
- Duk da tsananin fafatawar da aka yi, rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar ba su taba talakawan garin ba, illa dai jami'an tsaron da suka tunkara
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kwara – An shiga tashin hankali a garin Kemanji da ke ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara, biyo bayan wani hari da ƴan bindiga suka kai wa sansanin sojoji a daren jiya Litinin, 20 ga watan Afrilu, 2026.
Harin wanda aka kai da misalin ƙarfe 3 na dare, ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji uku da kuma ƴan banga biyu.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kai farmaki fada, sun yi garkuwa da mai martaba Sarki a Najeriya

Source: Twitter
'Yan ta'adda sun kashe sojoji a Kwara
Ƴan bindigar, waɗanda aka ce sun kai harin cikin ayari, sun far wa sansanin ne wanda ke ɗauke da sojoji, masu gadin gandun daji, da kuma ƴan banga, in ji rahoton Daily Trust.
Baya ga kisan da suka yi, maharan sun yi nasarar ƙwace motar yaƙi ta sojoji, makamai, harsashi masu yawa, da kuma babura 12 mallakar jami'an tsaron.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa maharan sun fito ne daga dajin dajin nan na "Kainji National Park" inda suka nufi sansanin jami'an tsaron kai-tsaye.
Yadda maharan suka farmaki sojoji
Shugaban ƙauyen Kemanji, Alhaji Sanni Zikki, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewa an yi musayar wuta mai tsanani tsakanin ɓangarorin biyu.
"Sun shigo garin ne daga Kemanji da misalin karfe 3:00 na dare kuma suka farmaki sansanin jami'an tsaron. Sun kashe sojoji uku da 'yan banga biyu, yayin da wasu suka jikkata.

Kara karanta wannan
Alkawuran da Tinubu, Atiku da wasu da ke neman takarar shugaban kasa suka fara yi wa talakawa
"Sun kuma tafi da babura 12, motar yaki, bindigogi da alburusai."
A cewar mazauna garin, ƴan bindigar sun kwashe nasu mutanen da sojoji suka kashe ta hanyar amfani da motar sojojin da suka ƙwace, in ji rahoton The Sun.

Source: Original
Halin da wasu sojoji suke ciki
A halin yanzu, an kwashe sojoji da jami'an tsaron da suka ji rauni zuwa babban asibitin Kaiama domin ba su kulawa, yayin da waɗanda raunukan nasu suka yi tsanani aka garzaya da su asibiti a birnin Ilorin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa an tura ƙarin dakarun soji zuwa cikin dazuzzukan da ke kusa domin bin sawun maharan da kuma ƙoƙarin dawo da kayan yaƙin da aka sace.
'Yan bindiga sun sace sarki a Kwara
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Olayinka da ke ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara, Oba Salman Aweda.
Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kai hari fadar sarkin da tsakar dare, suka tafi da shi, matarsa da wani mutum daya.
Shugaban karamar hukumar Ifelodun, Hadji Abdulrasheed Yusufya ce jami'an tsaro sun baza komarsu a dazukan yankin domin ceto su.
Asali: Legit.ng