Jonathan Ya Yi Martani Mai Zafi bayan Atiku Ya Soki Gwamnatinsa
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Ebele Jonathan
- Goodluck Jonathan ya fito ya yi martani kan kalaman na Atiku, inda ya nuna cewa duk wani shugaba yana iya yin kuskure
- Tsohon shugaban kasar ya kuma haska wasu daga cikin manyan nasarorin da ya su lokacin da yake mulki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Dr Goodluck Jonathan, ya yi martani kan sukar da Atiku Abubakar ya yi masa.
Goodluck Jonathan ya kare gwamnatinsa, inda ya ƙara da cewa ya yi iya kokarinsa lokacin da yake kan mulki.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Jonathan ya bayyana hakan ne yayin yake jawabi a wurin taron karrama mambobin ƙungiyar tsofaffin jakadun Najeriya (ARCAN) na shekarar 2025 da aka yi a Abuja ranar Litinin, 20 ga watan Afirilun 2026.
Atiku ya ragargaji Jonathan
Martaninsa ya biyo bayan sukar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi wa gwamnatinsa.
Atiku, wanda ke neman takarar shugaban ƙasa ne a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya bayyana Jonathan a matsayin mara ƙwarewa, yana mai cewa ya tafka kurakurai lokacin da yake jan ragamar mulki.
Wane martani Jonathan ya yi?
Jonathan ya ce babu wanda zai zama gwamna ko shugaban ƙasa da zai ce bai yi kuskure ba.
“Don haka, ba a daɗe ba, wani babban ɗan siyasa ya ce, ‘Oh, Jonathan ya yi ƙuruciya da yawa kuma ƙila shi ya sa ya tafka kurakurai.’"
“Idan na yi kuskure, eh, babu wanda zai zama gwamna ko shugaban ƙasa da zai ce bai yi kuskure ba. Ko da kuwa ka ɗaukaka kanka zuwa matsayin abin bauta."
“Dukkan ɗan adam dole ne ya yi kuskure. Na zama shugaban ƙasa a shekarar 2010 ina ɗan shekara 53. Na bar mulki a 2015 ina ɗan shekara 58, sai su ce na yi ƙuruciya da yawa. Shin sai na kai shekara 100 ne kafin na gudanar da al’amuran ƙasa?”

Kara karanta wannan
Atiku ya kare kansa kan zargin cin hanci, ya tuna baya kan abin da Obasanjo ya yi maaa
- Goodluck Jonathan
Jonathan ya haska nasarar da ya samu
Tsohon Shugaban ya kare shawarwarin da ya ɗauka a ofis, yana mai cewa yayin da kuskure yake tabbatacce, shi dai ya yi iya ƙoƙarinsa.

Source: Twitter
Tsohon shugaban ya nuna nasarorin diflomasiyya da Najeriya ta samu a lokacin mulkinsa, musamman zaɓen ta da aka yi a matsayin mamba a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya.
“Ina magana ne da jakadu, don haka zan iya cewa a lokacina, na san abin da na yi domin mu bayyana a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya har sau biyu… Idan da ban san me nake yi ba, ba na jin zan iya nasarar bi ta wannan tsari."
- Goodluck Jonathan
An gargadi Jonathan kan yin takara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya samu gargadi kan batun sake tsayawa takara a zaben 2027.
Shugaban jam'iyyar ZLP na kasa, Dan Nwanyanwu ya gargadi Goodluck Jonathan da ya guji tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Nwanyanwu ya ce mutanen da suke zuga Jonathan ya tsaya takara su ne wadanda suka yi aikin kawar da shi a lokacin da yake mulki.
Asali: Legit.ng
