Alhakin Falasdinawa: Za a Cafke Benjamin Netanyahu a Kasar Hungary

Alhakin Falasdinawa: Za a Cafke Benjamin Netanyahu a Kasar Hungary

  • Péter Magyar da ya lashe zaben Firaminista a kasar Hungary ya yi alkawarin cafke Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a kasar shi
  • A makon da ya wuce ne Péter Magyar ya kayar da na hannun daman Shugaban Amurka, Donald Trump a zaben da aka yi a kasar Hungary
  • Kotun aikata manyan laifuffuka ta duniya (ICC) ce ta yi umarnin a cafke Benjamin Netanyahu saboda kashe kananan yara da mata a Gaza

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Hungary - Sabon firaministan da aka zaba, Péter Magyar, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cika dukkan wajibcin doka na kasa da kasa ta hanyar kama firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, idan ya shiga yankin Hungary.

Wannan bayani ya nuna babban sauyi daga tsohuwar gwamnati karkashin Viktor Orbán, wanda a baya ya rika kare Netanyahu daga matsin lamba na dokokin kasa da kasa tare da sukar cibiyoyin duniya.

Kara karanta wannan

Gumi ya magantu kan 'yan bindiga da sojojin Turkiyya ke shirin zuwa Najeriya

Péter Magyar da Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu a hagu, Péter Magyar a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton the Guardian ya nuna cewa ICC ta nemi a cafke Netanyahu ne saboda aikata laifuffukan yaki a kan mata da yara a yankin Gaza.

Za a kama Benjamin Netanyahu a Hungary

Da yake magana kan kudurin gwamnatinsa na bin dokokin kasa da kasa, Péter Magyar ya tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da rike Hungary a matsayin mamba mai aiki da kotun ICC.

Ya ce tawagar lauyoyinsa sun yi cikakken nazari kan lamarin kuma sun kammala cewa dole ne Hungary ta mutunta yarjejeniyoyin da ta rattaba hannu a kansu.

“Na bayyana a fili cewa Hungary na son ci gaba da zama mamba a kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya,”

In ji Magyar, yana mai karawa da cewa idan wanda ke karkashin sammacin neman kama shi daga ICC ya shiga yankin wata kasa mamba:

“Dole ne a kama shi.”

Ga bayanin da Magyar ya yi a bidiyon da Al Jazeera ta wallafa a X:

Kara karanta wannan

Amurka ta farmaki jirgin Iran a teku, China ta fitar da gargadi ga Trump

Dalilin neman kama Netanyahu

Sammacin kama Netanyahu na da alaka da fadan Hamas da isra'ila da ya fara a ranar 7 ga Oktoba, 2023 da kuma mummunar barnar da sojojin kasar suka yi a Gaza.

Kwamitin alkalai uku na ICC ya ce ya samu hujjoji masu karfi da ke nuna cewa Netanyahu da Yoav Gallant:

“Na da alhakin aikata laifin yaki na amfani da yunwa a matsayin makami, da kuma laifuffukan cin zarafin bil’adama da suka hada da kisa, tsanantawa da sauran ayyukan rashin jin kai.”
Mutanen Gaza yayin jana'iza
Mutanen Gaza sun dauko gawar dan uwansu da Isra'ila ta kashe. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bugu da kari, kwamitin ya ce akwai hujjoji masu karfi da ke nuna cewa suna da laifi a matsayin manyan shugabannin kan yaki na kai hari kai tsaye ga fararen hula.

Péter Magyar ya lashe zabe

A wani labarin, mun kawo muku cewa a farkon watan Afrilun 2026 Péter Magyar ya kifar da abokin Donald Trump, Viktor Orbán a zaben Hungary.

Kara karanta wannan

An budewa jirgin Faransa wuta da zai wuce ta Hormuz da Iran ta toshe

Amurkawa da dama sun barke da murna kan kifar da Viktor Orbán da aka yi, suna cewa duniya ta gaji da 'yan kama karya a duk inda suke.

A daya bangaren kuma, attajirin duniya, Elon Musk ya yi alhinin rasa mukamin Firaminista da Viktor Orbán ya yi duk da yana da sabani da Trump.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng