Bidiyo: Yadda Babban Hadimin Tinubu ke Zuga Su Nafiu Bala Su Tarwatsa ADC
- Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya yi kalaman da suka tayar da kura game da jam'iyyar adawa ta ADC
- A wani bidiyo, an hango Femi Gbajabiamila yana kira ga Nafiu Bala da ya ke ikirarin zama shugaban ADC ya tsaya a jam'iyyar ya jawo matsala
- Hakan na zuwa ne yayin da bangaren David Mark ke zargin cewa ana amfani da su Nafiu Bala wajen kawowa 'yan adawa cikas a zaben 2027
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An samu suka da dama a kafafen sada zumunta bayan kalaman shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, wanda ya bukaci dan majalisar wakilai, Hon. Leke Abejide, da ya zauna a ADC ya tarwatsa ta.
Rahotanni sun nuna cewa ADC na cikin rikici a halin yanzu, inda bangarori daban-daban ke fafatawa domin kwace iko da shugabancin jam’iyyar.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa Gbajabiamila wada tsohon shugaban majalisar wakilai ne ya yi wannan bayani ne a bikin cika shekaru 50 na matar Abejide a Abuja.
Kira a tarwatsa ADC a Najeriya
Wani bidiyon taron da ya bayyana a intanet ya nuna Gbajabiamila yana karfafa wa dan majalisar, wanda ke bangaren Nafiu Bala na ADC, da ya ci gaba da zama a cikin jam’iyyar tare da kara kaimi a rikicin cikin gida.
A cikin bidiyon da ya yadu, Gbajabiamila ya ce:
“Na san ka a matsayin dan jam’iyya mai kishi. Na san ka a matsayin mayaki. Na san kai mutum ne da ba ya son a zalunce shi. Don haka rokon da nake maka shi ne ka zauna a ADC. Ka yake su.
"Ka tarwatsa su. Ka rike jam’iyyarka ADC. Kada ka bar su."
“Muna son abin da kake yi. Ka ci gaba. Kada ka damu da abin da tsohon gwamnan ya ce za su zo su shiga APC. A’a, a’a, a’a. Ka zauna a ADC. Ka yi tazarce a ADC, kuma za ka yi.
"Ka kawo Gombe, menene sunansa ma? Bala Gombe. Ka kawo shi. Ka yi abin da ya dace. Kai mayaki ne. Ka yi abin da ya dace.
Babu wanda zai zo ya kwace maka jam’iyyarka. Jam’iyyar da ka gina da guminka. Ka ci gaba. Allah ya ba ka sa’a a kotu.”

Source: Facebook
Martanin 'yan Najeriya kan rusa ADC
Wadannan kalamai sun haifar da suka a intanet, inda ‘yan Najeriya da dama suka zargi jam’iyyar APC da jawo katsalandan a siyasa da kuma tayar da rikici a cikin jam’iyyun adawa.
A dandalin X, mutane sun nuna fushi kan kalaman Gbajabiamila, suna bayyana su a matsayin marasa bin ka’idojin dimokuradiyya da kuma rashin hikima a siyasa.
Wani mai mai suna Lapai Boy ya rubuta:
“Ba za su ci gaba da zama jam’iyya mai mulki har abada ba, komai zai yi karshe watarana.”
Oluwadamilare ya ce:
“Abin kunya… wannan mutumin da ake kira Abejide yana da masu masa fada… babu wanda zai ba shi shawara? Yana yaki da dimokuradiyya.”
Matthew Beckley ya kara da cewa: “APC na tunanin 2027 za ta zama kamar 2023 ne, idonsu za su bude a gaba.”
Ga bidiyon maganar da Gbajabiamila ya yi da Leadership ta wallafa a X.
Shekarau ya koma APC daga PDP
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya sanar da ficewar shi daga jam'iyyar PDP.
Biyo bayan haka, Shekarau ya koma jam'iyyar APC mai mulki inda ya bayyana cewa zai hada kai da gwamna Abba Kabir Yusuf a Kano.
A wata sanarwa da ya fitar, gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi maraba da Malam Ibrahim Shekarau, inda ya ce ya yi tunani mai matukar kyau.
Asali: Legit.ng


