Minista a Gwamnatin Trump Ta Bar Mukaminta yayin da Yake Ci Gaba da Barazana ga Iran

Minista a Gwamnatin Trump Ta Bar Mukaminta yayin da Yake Ci Gaba da Barazana ga Iran

  • Gwamnatin kasar Amurka, karkashin jagorancin Shugaba Donald Trump, ta rasa daya daga cikin ministocinta
  • Ministar kwadago, Lori Chavez-DeRemer, ta yi murabus daga mukaminta, inda za ta koma aiki a wani bangaren
  • Tuni Daraktar yada labarai na fadar White House ta sanar da wanda zai ci gaba da rike ma'aikatar a matsayi na wucin gadi

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Ministar kwadagon Amurka, Lori Chavez-DeRemer, ta yi murabus daga Gwamnatin Donald Trump.

Ministar ta bar Gwamnatin Trump ne domin karbar aiki a kamfanoni masu zaman kansu, a daidai lokacin da ake gudanar da bincike na cikin gida kan zargin rashin da'a.

Lori Chavez ta bar gwamnatin Donald Trump
Lori Chavez-DeRemer da Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Win McNamee, Andrew Harnik
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa daraktan sadarwa a fadar White House, Steven Cheung, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Ministar kwadago ta bar gwamnatin Trump

Kara karanta wannan

Magana ta kare, tsohon gwamnan jihar Kano, Shekarau ya fice daga jam'iyyar PDP

“Ministar kwadago Lori Chavez-DeRemer za ta bar gwamnati domin karbar wani matsayi a kamfanoni masu zaman kansu."
“Ta yi gagarumin aiki a mukaminta ta hanyar kare ma’aikatan Amurka, aiwatar da kyawawan ayyukan kwadago, da kuma taimakawa Amurkawa samun karin kwarewa don inganta rayuwarsu.”

- Steven Cheung

Steven Cheung ya kara da cewa Keith Sonderling ne zai yi aiki a matsayin ministan wucin gadi na ma’aikatar kwadago.

Lori Chavez-DeRemer ta yi godiya

A cikin wata sanarwa a shafinta na X, Chavez-DeRemer ta rubuta cewa:

"Abin farin ciki ne da alfahari a yi aiki a wannan gwamnati mai tarihi da kuma yi wa babban Shugaban kasa a rayuwata aiki.”
“Ina alfahari da cewa mun samu gagarumin ci gaba wajen ciyar da manufar Shugaba Trump gaba na dinke baraka tsakanin ‘yan kasuwa da 'yan kwadago da kuma sanya ma’aikatan Amurka a gaba a ko yaushe."

Akwai zarge-zarge a kan tsohuwar ministar

Tashar CNN ta ce gajeren wa’adin mulkin Chavez-DeRemer ya kasance cike da hargitsi yayin da take fuskantar bincike na cikin gida biyo bayan korafe-korafe a cikin ma’aikatar game da halayenta.

Kara karanta wannan

Saraki ya jefi gwamnatin Buhari da zargi kan fashin Offa, ya fallasa gwamnan Kwara

An taba bayar da rahoton cewa an haramta wa mijinta shiga babban ofishin ma’aikatar sakamakon zargin cin zarafin mata. An rufe binciken manyan laifuffuka kan wannan batu.

Ministar kwadagon Amurka ta yi murabus
Ministar kwadagon Amurka, Lori Chavez-DeRemer da ta yi murabus Hoto: Tom Williams
Source: Getty Images

A watan Maris, an tilasta wa biyu daga cikin manyan mataimakanta barin aiki a daidai lokacin da ake binciken rashin da'a a hukumar.

Tsawon watanni, ofishin babban sufeton ma’aikatar kwadago yana binciken wani korafi na cewa Chavez-DeRemer tana kwanciya da daya daga cikin jami’an tsaron dake kare ta.

Akwai sauran zarge-zargen halaye marasa dacewa, kamar tura ma’aikata su siyo mata giya da kuma kokarin amfani da tafiye-tafiyen aiki a matsayin uzurin tafiyar kashin kanta, kamar yadda wata majiya a ma’aikatar kwadago dake da masaniya kan lamarin ta bayyana.

Trump ya yi barazana ga Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya nuna kwarin gwiwar cimma yarjejeniya da Iran.

Donald Trump ya yi gargadin cewa idan hakan ba ta faru ba, ƙasar za ta fuskanci matsaloli masu tsanani fiye da duk abin da ta taɓa gani a baya.

Hakazalika, Trump ya yi gargaɗi mai tsauri kan batun makaman nukiliya, yana cewa bai kamata a bari Iran ta samu damar mallakar irin wannan makami ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng