APC Ta Sa Ranar Zaɓen Fitar da Gwani, Ta Saka N100m na Neman Takarar Shugaban Kasa
- Shirin tunkarar babban zaɓen 2027 ya fara kankama yayin da jam'iyya mai mulki ta APC ta fara fitar da jadawalin fitar da ƴan takara
- Jam'iyyar APC ta sanya 15 zuwa 16 ga Mayu na shekarar 2026 domin zaɓen fitar da gwani na kujerar shugaban ƙasa
- Farashin fam ya kai N100m ga masu neman takarar shugaban ƙasa yayin da aka fitar da farashin sauran mukamai a ƙarƙashin APC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam’iyyar APC ta ayyana ranakun 15 da 16 ga watan Mayu na shekarar 2026 domin gudanar da zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa, a wani muhimmin mataki na shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
Jadawalin da APC ta fitar ya kunshi muhimman matakai daga sayar da fam zuwa gudanar da zaɓukan fitar da gwani a dukkannin muƙaman siyasa.

Kara karanta wannan
"Mun ba ku awanni 72": Boko Haram ta yi wa gwamnati rashin kunya bayan sace mutum 416 a Borno

Source: Facebook
Channels TV ta wallafa cewa jadawalin, wanda jam’iyyar ta fitar na ɗauke da sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren tsare-tsaren APC na ƙasa, Sulaiman Argungu.
APC ta fitar da jadawalin fitar da gwani
Jaridar Punch ta wallafa cewa a cewar jadawalin, za a fara sayar da fam ɗin nuna sha’awar tsayawa takara daga ranar 25 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu, 2026
Haka kuma an umarci waɗanda za su sayi fam ɗin da cewa ranar ƙarshe da ake buƙatar su miƙa fam ita ce 4 ga Mayu na shekarar 2026.
Za a tantance masu neman takara daga ranar 6 zuwa 8 ga Mayu, 2026 sannan a fitar da sakamakon tantancewar a ranar 11 ga Mayu, 2026.
Bayan haka, za a buɗe ƙofar ɗaukaka ƙara daga ranar 12 zuwa 13 ga Mayu na shekarar 2026 ga waɗanda ke ganin ba a yi masu dai-dai ba.
Yadda jam'iyyar APC ta tsara fitar da gwani

Kara karanta wannan
"Wasun su hotiho ne": Tsohon dan majalisa ya gargadi Tinubu kan dogaro da gwamnoni a 2027
Game da sauran muƙamai, jam’iyyar ta tsara cewa za a gudanar da zaɓen fitar da gwani na majalisar wakilai a ranar 18 ga Mayu, 2026.
Za a yi zaben majalisar dattawa a ranar 20 ga Mayu, 2026 sai na majalisun jihohi a ranar 21 ga Mayu, 2026 yayin da na gwamnonin jihohi zai gudana a ranar 23 ga Mayu, 2026.
Jam’iyyar ta bayyana cewa jimillar kuɗin fam ga masu neman takarar shugaban ƙasa ya kai Naira miliyan 100, wanda ya haɗa da N30m na fam ɗin nuna sha’awa da kuma N70m na fam ɗin tsayawa takara.

Source: Twitter
Masu neman takarar gwamna kuwa za su biya Naira miliyan 50, yayin da na sauran muƙamai kamar sanatoci, ‘yan majalisar wakilai da na jihohi suka bambanta.
Sai dai APC ta yi rangwame ga mata, matasa da masu nakasa, inda ta ce za su biya kuɗin fm ɗin nuna sha’awa ne kawai tare da rabin kuɗin fom ɗin tsayawa takara
Jam’iyyar ta jaddada cewa an tsara wannan jadawali ne bisa kundin tsarin mulkin Najeriya, dokar zaɓe ta 2026 da kuma ƙa’idojin hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC).
Jam'iyyar APC ta kuma yi alƙawarin gudanar da sahihin zaɓen fitar da gwani mai domin ƙarfafa dimokuraɗiyyar cikin gida wanda zai karfafa tsarin a Najeriya baki daya.
An ja kunnen Tinubu kan gwamnonin APC
A baya, mun wallafa cewa tsohon sanata daga jihar Taraba, Abubakar Yusuf ya gargadi shugaban kasa Bola Tinubu da kada ya dogara da gwamnonin APC a zaɓen 2027.
Tsohon Sanatan Taraban ya bayyana haka ne yayin da APC ta tara gwamnonin adawa da suka sauya sheka cikinta gabanin babban zaben 2027 mai gabato wa.
Sanata Abubakar Yusuf, wanda jigo ne a APC ya yi gargadi da cewa wasu daga cikin gwamnonin ba su da ƙarfi a matakin ƙasa domin jawo kuri’un da Tinubu ke bukata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
