Latest
Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mike Okiro, ya zargi gwamnatin tarayya da raunana rundunar ‘yan sanda, yana cewa hakan ya ƙara matsalar tsaro a Najeriya.
Barrista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya ce shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa aikata laifuka da rikicin ƙungiyoyin daba a jihar.
'Yan bindiga sun kashe Kanal Abdussalam Ude a birnin Abuja, yayin da matarsa, direbansa da jami'in tsaronsa suka jikkata. Ana ci gaba da bincike.
Hukumar Federal Character Commission ta bayyana kura-kurai guda bakwai da ke hana masu neman aikin gwamnati samun nasara, tare da gargadin su guji masu damfara.
Jam'iyyar APC ta kaddamar da kwamitin yakin neman zaben gwamnan Osun na 2026, tana mai bayyana zaben a matsayin gwajin shirin da take yi domin babban zaben 2027.
Sanata Oluremi Tinubu ta ce babu wani ɗan Najeriya da ya kamata ya kwana da yunwa yayin da gwamnatin tarayya ke faɗaɗa shirin tallafa wa masu buƙata.
Rahoto ya nuna cewa kusan 29% na malaman makarantu a Borno na fuskantar matsanancin damuwa, lamarin da ke sanya su tunanin barin aikin koyarwa a jihar.
Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce za a ɗora wa Shugaba Bola Tinubu alhakin duk wani abu da ya samu Nasir El-Rufai, yana zargin an tsare shi ne saboda siyasa.
Fadar Shugasa ta ce wa'adin shekara huɗu da Mr. Peter Obi ya amince da shi zai tauye burin Igbo na shugabancin Najeriya, ta kuma bayyana dalilanta.
Masu zafi
Samu kari