Sarkin Musulmi Ya Yi Fatali da Jitar Shirin Maida Najeriya Kasar Musulunci
- Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya musanta rade-radin cewa ana shirin musuluntar da Najeriya
- Sultan ya jaddada cewa Musulmi ba su da wata manufa ta kawar da Kiristoci, yana mai cewa Allah cikin hikimarsa ya hada addinan biyu a wuri daya
- Sarkin ya kuma yi Allah-wadai da danganta laifuffukan ta’addanci da addini, yana mai cewa ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ba su da alaka da musulmi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya karyata rade-radin cewa ana shirin musuluntar da Najeriya.

Kara karanta wannan
Bayan abin da ya faru, an haramta wa masu digirin girmamawa amfani da 'Dr' a Najeriya
Mai Alfarma Sarkin Musulmin ya bayyana irin wannan magana a matsayin abin da ba zai yiwu ba, wanda aka kirkira da nufin raba kan al’umma.

Source: Getty Images
Sarkin Musulmi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a taron farko na Majalisar Tattaunawar Addinai ta Najeriya (NIREC) da aka gudanar a Abuja, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Da gaske ana shirin musuluntar da Najeriya?
Sultan ya jaddada cewa Musulmi ba su da wata manufa ta kawar da Kiristoci, yana mai cewa Allah ne da hikimarsa ya hada addinan biyu domin wami dalili da ba wanda ya sami.
Sarkin, wanda shi ne shugaban haɗin gwiwa na NIREC, ya ce majalisar na ci gaba da zama muhimmin dandali na tattaunawa, wanda ya bayyana a matsayin hanya mafi dacewa don warware matsalolin ƙasa.
Ya kuma ce a tsawon shekaru 20 da ya yi a cikin majalisar, bai taba rasa halartar wani taro ba, abin da ya nuna jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya.
“Muna ganin tattaunawa da juna ta fi mu rika fada tsakaninmu, mu fahimci bambance-bambancenmu, sannan mu yi ƙoƙarin kawar da su; ni Musulmi ne, kai Kirista ne, dole mu zauna tare cikin girmamawa,” in ji shi.
Sarkin Musulmi ya gargadi malamai
Tribune Nigeria ta ruwaito cewa da yake magana kan batun fahimtar addini, Muhammad Sa'ad Abubakar ya yi gargadi kan karuwar malamai na bogi da ba su da zurfin ilimi a addini.
Ya bayyana cewa iya harshen Larabci ba ya nufin mutum malamin Musulunci ne, kamar yadda ya ce akwai fastoci a wasu sassan Gabas ta Tsakiya da ke wa’azi da Larabci.
Ya bukaci shugabannin addinai su kasance masu ilimi sosai domin su jagoranci mabiyansu yadda ya kamata tare da hana amfani da addini wajen son zuciya ko manufofin siyasa.

Source: Facebook
Musulmai na da hannu a ta'addanci?
Sarkin ya kuma yi Allah-wadai da danganta laifuffukan ta’addanci da addini, yana mai cewa ya kamata a kira ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da sunansu ba tare da alakanta su da Musulunci ba.
Ya jaddada cewa duk wanda ya kashe mutum mara laifi da sunan addini, “wuta ce makomarsa,” domin Musulunci ya dauki kashe mutum daya tamkar kashe dukkan bil’adama.

Kara karanta wannan
Matar da APC ta tsaida takara a Katsina ta fara fuskantar cikas daga malaman Musulunci
Sultan ya ja hankali kan matasa
A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Musulmin ya nuna illar da ke tattare da yin watsi da matasa wadanda ke rayuwa a cikin al'umma ba tare da samar musu da abin dogaro da kai ba.
Ya ce zuba jari wajen ƙarfafa matasa ta hanyar koyon sana’o’i, kasuwanci da tsarin ba da jagoranci, na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya.
Sarkin Musulmin ya bayyana cewa matasan da ba su da aiki kuma suke cikin takaici sun fi saurin faɗa wa cikin laifuffuka da sauran munanan ɗabi’u.
Asali: Legit.ng
