Babbar Sallah: Gwamnati Ta Kayyade Farashin Dabbobin Layya a Daular Larabawa
- Hukumar IACAD ta Dubai ta amince da ƙayyadadden farashin dabbobin layya na shekarar 2026 domin kauce wa tsadar da ba ta dace ba
- Farashin dabbobin ya fara ne daga Dirham 350 zuwa Dirham 800, ya danganta da nau'in dabba da kuma inda za a gudanar da yanka da rarrabawa
- Ana sa ran yin sallar layya ta shekarar 2026 a ranar 27 ko 28 ga watan Mayu, abin ya danganta da ranar da aka ga jinjirin watan Zul Hijjah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Dubai - Yayin da Musulmai a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ke shirye-shiryen sallar layya ta shekarar 2026, hukumomin addinin Musulunci a birnin Dubai sun amince da farashin dabbobin layya (Qurbani) a bana.
An ɗauki wannan matakin ne domin taimaka wa wajen rage bambancin farashi, tare da tabbatar da gaskiya da fayyace lamura ga masu son bayar da tallafi yayin da suke yanke shawarwari.

Source: Getty Images
Tsarin kayyade farashin dabbobi a Dubai
Hukumar Kula da Al’amuran Musulunci da Ayyukan Jinƙai ta Dubai (IACAD) ta bayyana waɗannan sababbin farashi ne tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin agaji da cibiyoyin da aka amince da su, in ji rahoton Gulf News.
Rahotanni sun nuna cewa an tuntubi masu samar da dabbobin layya da aka amince da su, sannan an bi ƙa’idoji na musamman don tabbatar da cewa iyalai marasa galihu, ko dai a cikin UAE ko a ƙasashen waje, sun amfana da naman layyar.
Hukumar IACAD ta bayyana cewa:
“Amincewa da waɗannan farashin na zuwa ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin hukumar na ganin an daidaita farashin kudin sayen dabbobin layya a tsakanin ƙungiyoyin agaji da aka amince da su.”
Hukumar ta ƙara da cewa:
“Hakan yana taimakawa wajen inganta sarrafa albarkatu da tabbatar da adalci, tare da ƙoƙarin ganin cewa tallafin naman layyan ya isa ga waɗanda suka dace da shi."

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali a Filato, ƴan bindiga sun kashe gomman mutane a sabon hari
Jadawalin farashin dabbobin layya
IACAD ta sake jaddada jajircewarta na samar da ayyuka masu sauƙi da tsari waɗanda ke haɓaka tsarin ayyukan jinƙai a birnin, daidai da dabarun Gwamnatin Dubai na cimma dorewar ci gaban al’umma.
Ga yadda jadawalin farashin yake a hukumance:
- Farashin dabba a ƙasar da aka samo ta: Dirham 350 (Yanka da rarrabawa a ƙasashen waje).
- Dabba daga Kenya ko Habasha: Dirham 490 (Yanka a ƙasashen waje, rarrabawa a cikin UAE).
- Dabba daga Somaliya: Dirham 800 (Yanka da rarrabawa a cikin UAE).
Ana shawartar masu ba da tallafi da su gudanar da ibadar layyar su ta hanyar amintattun hanyoyin agaji waɗanda ke da rAjista da Dubai domin tabbatar da cewa naman ya isa ga waɗanda suka dace.

Source: Original
Ranar sallar Layya ta 2026
Bisa ga lissafin falaki na Kwalejin Falaki ta Sharjah, sallar layya, wadda ke faɗawa ranar 10 ga watan Zul Hijjah a kowace shekara, za ta kasance ne a ranar Laraba, 27 ga watan Mayu.
Sai dai kuma, tun da yake kalandar Musulunci tana bin yanayin wata ne, ainihin ranar fara kowane watan Hijri ya dogara ne da ganin jairin wata. A ƙasar UAE, za a nemi ganin watan Zul Hijjah a ranar 17 ga watan Mayu.
Idan ba a ga jairin watan ba a ranar, watan Zul Hijjah zai fara ne a ranar 19 ga watan Mayu, sannan ranar Idi za ta kasance a ranar Alhamis, 28 ga watan Mayu.
Farashin raguna a Katsina
Legit Hausa ta tuntubi Yusha'u Bello Kamfani, wanda ke sana'ar saye da sayar da dabbobi a karamar hukumar Faskari, jihar Katsina, ya shaida mana cewa:
"Ya danganta gaskiya, kudi kudi ce, babba har N300,000, N250,000, N280,000, ya danganta dai da wadda ake so, amma babba mai kyau sai ta haura N20,000.
"Sai dai akwai kasa da haka, har na kasa da N100,000 ana samu, ko ni ranar Asabar kasuwar Dandume na sayar da tunkiyar N95,000."
"A guji cin bashi don sayen ragon layya"
A wani labari, mun ruwaito cewa, babban limamin jami'ar LASU, Farfesa Amidu Sanni ya shawarci Musulmi su gujewa cin bashi don sayen dabbar layya.
Malamin ya ce duk wanda bai da sararin yin layya, to wajibcin ya faɗi a kansa, yana mai cewa bai kamata mutane su jefa kansu a matsala ba.
Farfesa Sanni ya bukaci shugabanni tun daga Bola Tinubu har ciyamomin kananan hukumomi su yi duk mai yiwuwa wajen saukakawa talakawa.
Asali: Legit.ng

