Kafin Uba Sani da El Rufa'i, Pantami Ya Yi wa Sarakuna Sulhu da Buhari

Kafin Uba Sani da El Rufa'i, Pantami Ya Yi wa Sarakuna Sulhu da Buhari

  • Tsohon ministan sadarwa na kasa, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi karin bayani kan sulhun da ya yi wa gwamnan Kaduna, Uba Sani da Nasir El-Rufa'i
  • Pantami ya ce ba wannan ne karon farko da ya fara sulhu ba, inda ya fadi yadda ya sansanta marigayi Muhammadu Buhari da wasu sarakuna
  • Malamin ya yi karin bayani ne bayan sukar da jama'a suka yi game da yadda ya yi kokarin sasanta Uba Sani da El-Rufa'i a makabarta a Abuja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Malamin addinin Musulunci kuma tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi karin bayani kan sulhun da ya yi wa Uba Sani da Nasir El-Rufa'i.

Malamin ya bayyana hadarin da ke cikin barin abokai ko 'yan uwa su shafe lokaci mai tsawo ba tare da magana da juna ba.

Kara karanta wannan

"Zai fi na baya"; Donald Trump ya sake yin babbar barazana ga Iran

Sheikh Isa Ali Pantami a Abuja
Sheikh Isa Ali Pantami yana wa'azi a masallacin Annor a Abuja. Hoto: Profesor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa Sheih Isa Ali Pantami ya yi magana ne kan sulhun a wata hira da BBC Hausa da tashar ta wallafa a X.

Batun sulhun Uba Sani da El-Rufa'i

Game da sulhun da Sheikh Pantami ya yi wa Uba Sani da El-Rufa'i, ya ce ya yi sulhun ne saboda yadda addini ya koyar da hakan.

Pantami ya sanar da cewa bai yi kokarin sanin me ya jawo rikicin ba, ya yi kokarin ne kawai domin sasanta tsakanin su a matsayinsu na Musulmai.

A kan yi musu magana a makabarta kuwa, Pantami ya kara da cewa wasu manyan mutane sun yi kokarin ganin an hada Uba Sani da El-Rufa'i domin masu sulhu amma abin ya gagara.

Biyo bayan lamarin, Pantami ya sanar da cewa ya samu yabo daga wasu manyan mutane a Najeriya a kan kokarin sasanta Uba Sani da El-Rufa'i.

Pantami: Sulhun sarakuna da Buhari

Kara karanta wannan

Takarar gwamna: Sheikh Isa Pantami ya yi maganar sauya sheka daga APC

Sheikh Pantami ya bayyana cewa ba wannan ne karon farko da ya fara sulhu ba, domin ya sasanta marigayi Muhammadu Buhari da wasu sarakuna.

Malamin ya buga misali da yadda ya yi sulhu tsakanin marigayi shugaba Muhammadu Buhai da mai alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar III.

"A boye ne, na yi ta kaikawo tsakaninsu domin a samu sulhu don abu ya gyaru, tun ba su haduwa da juna har suka fara haduwa suna magana aka yi zama aka yafewa juna, ba kowa ya sani ba."

Ya kara da cewa ya yi sulhu tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II a shekarun ba.

Isa Ali Pantami da Muhammadu Buhari
Isa Ali Pantami da Muhammadu Buhari a Kaduna. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Ga bayanin da Pantami ya yi a bidiyo a kasa:

Batun takarar Pantami a Gombe

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya yi Allah wadai da yadda jam'iyyar APC ta fitar da 'yan takara a jihar Gombe.

Duk da cewa yana cikin wadanda suka saye fom din nuna sha'awar takara, Pantami ya bayyana cewa ba a zauna da shi ba wajen fitar da 'yan takara.

Malamin ya jaddada cewa zai yaki zaluncin da aka yi a jihar sai inda karfinsa ya kare domin tattabar da an yi adalci a cikin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng