Bayan Zarginsa da Shirin Tsige Obasanjo, Atiku Ya Mayar da Zazzafan Martani

Bayan Zarginsa da Shirin Tsige Obasanjo, Atiku Ya Mayar da Zazzafan Martani

  • Atiku Abubakar ya yi watsi da zargin cin hanci da Olusegun Obasanjo ya yi masa lokacin da suke mulkin kasa a Najeriya
  • Dan siyasar ya ce bai dace a jingina irin wannan zargi ga marigayi Ghali Umar Na'Abba ba, domin ba ya raye don kare kansa ko ƙaryata zargin
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce hankali ya kamata ya koma kan matsalolin tattalin arziki, tsaro da yunwa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi martani ga Olusegun Obasanjo

Atiku ya yi watsi da sabon zargin da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi masa kan yunkurin tsige shi.

Atiku ya yi zazzafan martani ga Obasanjo
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar da Olusegun Obasanj. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Matanin Atiku ga kalaman Obasanjo

A cikin sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce zargin ba wa marigayi Ghali Umar Na'Abba cin hanci abin takaici ne, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya fallasa yadda Atiku ya kitsa yunkurin tsige shi daga mulki

Atiku ya ce zargin wani yunƙuri ne na sauya tarihin siyasa da kuma bai wa ɗan takarar da Obasanjo ke goyon baya wata fa'ida kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ya ce bai dace a jingina irin wannan zargi ga mutumin da ya rasu ba, domin ba ya da damar kare mutuncinsa ko ya amsa abin da ake zarginsa da shi.

Atiku ya tambaya cewa idan zargin gaskiya ne, me ya sa Obasanjo bai bayyana shi ba tun lokacin da marigayi Na'Abba yake raye har zai iya tabbatarwa ko musanta shi.

Ya ƙara da cewa al'adar Afirka tana koyar da mutunta waɗanda suka rasu, don haka bai dace a jawo sunansu cikin rigingimun siyasa ba.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce babu wani hukuncin kotu ko wata hukuma da ta tabbatar da zargin cin hancin da ake masa.

Ya ce idan da akwai hujjojin aikata laifi, ya kamata gwamnatin da ke da cikakken iko a lokacin ta ɗauki matakin shari'a maimakon jira shekaru masu yawa.

Atiku ya bayyana cewa lokacin da aka sake fito da zargin ya nuna yana da alaƙa da siyasar zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya tsame kansa kan zargin kifar da tsohon gwamna, ya saka sunan Atiku

Ya ce manufar zargin ita ce bata masa suna da kuma bai wa wani ɗan takara fa'idar siyasa, amma ya ce 'yan Najeriya sun san gaskiya.

Atiku ya ce sabanin da ke tsakaninsa da Obasanjo ya samo asali ne daga adawarsa da yunƙurin wa'adi na uku, inda ya zaɓi kare kundin tsarin mulki.

Ya ce ba zai bari tsofaffin saɓanin siyasa su dauke masa hankali daga matsalolin da Najeriya ke fuskanta ba, musamman tsadar rayuwa, rashin tsaro, rashin aikin yi da yunwa.

Ya kuma ce Obasanjo na da 'yancin goyon bayan duk wanda yake so a zaɓen 2027, amma ya kamata ya bayyana hakan a fili ba tare da amfani da zarge-zargen da ba za a iya tabbatar da su ba.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.