Ta Yi Tsami: An Fallasa yadda Saudiyya Ta Rusa Shirin Trump na Tura Sojoji Hormuz

Ta Yi Tsami: An Fallasa yadda Saudiyya Ta Rusa Shirin Trump na Tura Sojoji Hormuz

  • Shugaba Donald Trump ya dakatar da "Project Freedom" bayan ƙasar Saudiyya ta hana Amurka amfani da sararin samaniyarta da sansanonin sojanta
  • Trump ya sanar da kaddamar da Project Freedom ne da nufin tura sojojin Amurka zuwa Hormuz domin yi wa jirage rakiya don kare su daga sojojin Iran
  • Sai dai, matakin na Saudiyya ta dauka ya rusa shirin Trump, wanda ya tilasta wa shugaban na Amurka yin amai da lashe wa kan tura sojoji zuwa Hormuz

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Rahoto ya bayyana wani babban dalili da ya 'tilasta wa' Shugaba Donald Trump dakatar da shirin tura sojojin Amurka zuwa mashigar ruwan Hormuz.

An gano cewa Trump ya fasa taimaka wa jiragen ruwa su ratsa ta mashigar Hormuz ne biyo bayan matakin Saudiyya na hana sojojin Amurka amfani da sansanoni da sararin samaniyarta.

Kara karanta wannan

"Zai fi na baya"; Donald Trump ya sake yin babbar barazana ga Iran

Saudiyya ta hana Amurka amfani da sansanoninta wanda ya tilasta Trump dakatar da shirin tura sojoji zuwa Hormuz.
Shugaban Amurka, Donald Trump tare da Yariman Saudiyya, Muhammad bin Salman, suna tattaunawa a Washington, DC. Hoto: Chip Somodevilla/Getty Images
Source: Getty Images

Saudiyya ta hana Amurka amfani da sansanoninta

Wasu jami'an Amurka biyu sun shaida wa NBC News cewa Trump bai tuntubi ƙawayen Amurka na yankin Gulf lokacin da zai sanar da fara shirin "Project Freedom" a ranar Lahadi ba, lamarin da ya fusata Saudiyya.

A matsayin martani, Masarautar Saudiyya ta sanar da Amurka cewa ba za ta bar sojojinta su tashi da jirage daga sansanin Prince Sultan da ke kudu maso gabashin Riyadh ba.

Hakazalika, Saudiyya ta sanar wa Trump cewa ba za ta bari sojojin Amurka su bi ta sararin samaniyarta don tallafa wa wannan shirin ba.

Wani kiran waya tsakanin Trump da Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman bai iya warware matsalar ba, wanda hakan ya tilasta wa shugaban dakatar da aikin domin dawo da damar amfani da sararin samaniyar yankin.

Tasirin hakan ga masu ruwa da tsaki a Gulf

Rahoton ya nuna cewa sauran kawayen Amurka a Gulf sun nuna mamakinsu na yadda Trump zai dauki wannan mataki ba tare da sanar masu ba. An ce Trump ya tattauna da shugabannin Qatar ne kawai bayan da aikin ya riga ya fara kankama.

Kara karanta wannan

Bayan abin da ya faru, an haramta wa masu digirin girmamawa amfani da 'Dr' a Najeriya

Wata majiya daga Saudiyya ta bayyana cewa Trump da Yariman Saudiyya suna tuntuɓar juna akai-akai, haka kuma jami'an Saudiyya suna tuntuɓar mataimakin shugaban ƙasa JD Vance, da Ministan waje Marco Rubio, da kuma rundunar CENTCOM.

Majiyar ta Saudiyya ta bayyana cewa Masarautar tana matuƙar goyon bayan ƙoƙarin diflomasiyya na ƙasar Pakistan don kulla yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka don kawo ƙarshen yaƙin.

Trump ya dakatar da tura sojoji zuwa mashigar Hormuz.
Shugaba Donald Trump (hagu) da wasu jirage a kusa da mashigar Hormuz. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Halin da shirin Trump yake ciki yanzu

Sojojin Amurka sun riga sun fara jera jerin jiragen ruwa da dama a yankin Gulf domin ratsawa ta mashigar lokacin da aka dakatar da aikin, in ji rahoton Yahoo News.

Rundunar CENTCOM ta riga ta sanar da cewa wasu jiragen ruwa biyu masu tutar Amurka sun riga sun sami nasarar ratsa mashigar a matsayin wani ɓangare na aikin kafin dakatarwar.

A cikin saƙonsa, Trump ya bayyana cewa za a dakatar da aikin na ɗan gajeren lokaci domin ganin ko za a iya kammala da kuma sanya hannu kan yarjejeniyar da za ta warware yaƙin.

Trump ya fasa tura sojoji Hormuz

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Donald Trump ya dakatar da aikin bude mashigar Hormuz da karfi da ke da nufin jagorantar jiragen kasuwanci su ratsa ta wajen.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Trump ya hasala kan Iran, ya yi babbar barazana ga kasar Musulunci

Sanarwar da Donald Trump ya fitar ta zo ne sa’o’i kaɗan bayan Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce aikin yaƙi da Iran ya ƙare.

Wasu bayanai da aka samu daga jami'an gwamnatin kasar Iran ya nuna Tehran ta caccaki Donald Trump kan cewa ya ja da baya kan shirin da ya yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com