Rahoto: Jarumin Kannywood, Adam A Zango Ya Saki Matarsa Maimuna Pretty

Rahoto: Jarumin Kannywood, Adam A Zango Ya Saki Matarsa Maimuna Pretty

  • Rahotanni sun nuna cewa Jarumi Adamu A. Zango ya saki matarsa, Jaruma Maimuna Pretty, bayan aurensu ya shiga matsala
  • Bayan rabuwar auren, an ruwaito cewa Maimuna Pretty ta fara kwashe kayanta daga gidan da take zaune tare da Adam Zango
  • Majiyoyi sun ce an yi ƙoƙarin sasanta saɓanin da ya shiga tsakanin ma'auratan, amma duk ƙoƙarin sulhun bai kai ga nasara ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Kaduna - Rahotanni sun bayyana cewa fitaccen jarumin Kannywood, Adamu A. Zango, ya saki matarsa, jaruma Maimuna Pretty.

Bayanan da aka samu sun nuna cewa tsohuwar jaruma Maimuna ta fara kwashe kayanta daga gidan Adam A Zango bayan rabuwarsu.

Adam A Zango ya saki matarsa Maimuna Pretty
Jarumi Adam A Zango da Maimuna Pretty a lokacin bikin aurensu. Hoto: Fauziyya D. Suleiman
Source: Facebook

Adam A Zango ya saki matarsa Maimuna

Shafin Arewa Update ne ya fitar da rahoton mutuwar auren jarumi Adam A Zango da Maimuna Pretty a yammacin Juma'a, 31 ga Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ji zazzafan martani da ya tabo Kwankwaso, Obi a Kudancin Najeriya

Wasu makusantan ma'auratan sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce saɓani da ya shiga tsakaninsu ne ya haddasa rabuwar.

Majiyoyin sun ƙara da cewa an yi ƙoƙarin sasanta ma'auratan domin su warware matsalolin da ke tsakaninsu, amma hakan bai yi nasara ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Adamu A. Zango da Maimuna Pretty ba su fitar da wata sanarwa a hukumance domin tabbatar ko musanta rahotannin rabuwar aurensu ba.

Martanin mutane kan mutuwar auren Zango

Legit Hausa ta tattaro ra'ayoyin mutane game da wannan mutuwar aure na Adam A Zango:

Seeyama Shehu Baiti:

"Haka kuka zauna kuna yi ta zagin Maman Haidar har da cewa wai Zango ya yi hakuri da ita. To ai yanzu sai ku ci gaba."

Yusuf Muhammad:

"Gaskiya ko bai ma kamata ana ba Adam Zango aure ba."

Abdullahi Umar:

"Mai hali dai ba ya fasawa."

Usaini Usi:

"Tabbas ina tausayawa Zango, ka yi hakuri ka ci gaba da dogara ga Allah, Allah zai kawo ma mafita na alheri. Ka guji bayyanawa kowa damuwa in ba Allah ba."

Kara karanta wannan

INEC ta yi fatali da sanya sojoji a tsarin zaben Najeriya, an ji dalili

Karin ra'ayoyin 'yan social midiya

Muktar Dabo:

"In dai da gaske ne wallahi ni ma na rabu da kai har abada, ka zama mutumin banza kuma Allah ya isa tsakani na da kai."

Danladi Maineman Na Aure:

"Ya kamata hukumar Hisbah ta hana Adam A Zango aure."

Abdulkarim Muhd Sani:

"Ya auri Jamila Gwaska kawai ya huta wannan masifa da me tai kama."

Zainab Ishaq Muhammad:

"Allah shi ne ya san gaibu, amma tabbas akwai abin da ke damun Adamu, ko menene Allah ya yi ma magani, ya baka ikon cinye jarrabawa, ya inganta lafiya."

Suleiman Ibrahim:

"Ko fim din Kaddara a kan shi a kayi ne, dama an ce asali akan namiji ne, sai aka sauya zuwa mace."

Auren Adam Zango 7

Idan ba a manta ba, mun rahoto cewa Amina Uba Hassan (Maman Haidar) ita ce matar Adam A Zango ta farko, kuma mabudin aure-aure bakwai da jarumin ya yi a shekaru 19.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun shiga Kaduna da dare, sun kashe rayuka 30 sun kona gidaje

A kaf cikin mata shida da ya aura kafin aurensa na bakwai a 2025, Zango ya ce rabuwa da Safiyya Chalawa ne ya jefa shi a damuwa.

A wannan rahoton, Legit Hausa ta kawo muhimman abubuwan sani game da mata bakwai da jarumi Zango ya aura daga 2006 zuwa 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com