Houthi: Tinubu Ya Tsoma Najeriya a Yakin da ake da Masu Goyon bayan Iran

Houthi: Tinubu Ya Tsoma Najeriya a Yakin da ake da Masu Goyon bayan Iran

  • Saudiyya ta fara kafa ƙawancen ƙasashe na duniya domin kare manyan hanyoyin jiragen ruwa da ke jigilar ɗanyen mai daga hare-haren 'yan Houthi na Yemen
  • Ma'aikatar tsaron Saudiyya ta ce ƙasashe 14 ciki har da Najeriya sun amince da goyon bayan sabon ƙawancen da zai mayar da hankali kan tsaron Tekun Maliya
  • Matakin ya biyo bayan barazanar da Houthi suka yi na kakaba takunkumin zirga-zirgar jiragen ruwan Saudiyya a Tekun Bahar Maliya, lamarin da ya ƙara tayar da hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Riyadh, Saudiyya – Gwamnatin Saudiyya ta sanar da kafa wani sabon ƙawancen ƙasashe na duniya domin kare hanyoyin jiragen ruwa da ke jigilar ɗanyen mai daga hare-haren da 'yan Houthi ke kai wa.

An bayyana cewa ma'aikatar tsaron Saudiyya ta gudanar da taro da wakilan kusan ƙasashe 50 a birnin Riyadh domin tattauna hanyoyin tabbatar da tsaro a mashigar Bab al-Mandab, Tekun Bahar Maliya da kuma Tekun Aden.

Kara karanta wannan

Minista ya cire tsoro, ya fadi babban abin da ke rura wutar ta'addanci a Najeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da jakadan Saudi a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

RFI Hausa ta rahoto cewa ƙasashe 14 sun tabbatar da goyon bayansu ga wannan ƙawance, ciki har da Najeriya, Turkiyya, Masar, Pakistan da wasu ƙasashen Larabawa da Afirka.

Maganar da Pakistan ta yi

Ma'aikatar tsaron Saudiyya ta bayyana cewa sabon ƙawancen zai taimaka wajen kare hanyoyin kasuwanci da jigilar mai daga hare-haren da Houthi ke kai wa.

Haka kuma Pakistan ta yi Allah wadai da barazanar da Houthi suka yi na kakaba takunkumi kan zirga-zirgar jiragen ruwa a Tekun Bahar Maliya, tana mai cewa hakan ya saɓa wa ƙa'idojin dokokin ƙasa da ƙasa.

An bayyana cewa taron ya mayar da hankali kan yadda za a tabbatar da tsaro a ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin kasuwanci da jigilar makamashi a duniya.

Mai magana da yawun Houthi
Yahya Saree da ke magana da yawun Houthi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dalilin kafa sabon ƙawancen

Rahoton the Hill ya nuna cewa 'yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran sun yi barazanar hana jiragen ruwan Saudiyya zirga-zirga ta mashigin Bab al-Mandab.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta lallaba Saudiyya, tana so a taimaka wa Najeriya kan karatun allo

Sun bayyana hakan ne bayan wani hari da aka kai filin jirgin saman Sanaa da ke Arewacin Yemen, duk da cewa gwamnatin Yemen mai samun goyon bayan Saudiyya ta ɗauki alhakin kai harin.

Tun bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka da Iran a Fabrairun 2026, mahimmancin Tekun Bahar Maliya ya ƙaru saboda matsalolin da suka shafi mashigar Hormuz, inda ake jigilar ɗanyen man duniya sosai.

Tasirin hare-haren Houthi

Bayanan kamfanin Kpler sun nuna cewa zirga-zirgar jiragen dakon kaya ta Tekun Bahar Maliya ta ragu sosai sakamakon hare-haren Houthi.

A ranar Litinin, jiragen dakon kaya 11 ne kawai suka ratsa mashigar, wanda shi ne mafi ƙarancin adadi cikin watanni da dama.

Duk da hare-haren da Saudiyya ke kai wa yankunan da Houthi ke iko da su a Yemen, ƙungiyar ta ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa.

Remi ta zauna da Saudi

A wani labarin, mun ruwaito cewa matar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta buƙaci Saudiyya ta ƙara haɗin gwiwa da Najeriya wajen gyaran tsarin karatun Almajirai.

Ta ce inganta ilimin yara Almajirai zai taimaka wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta tare da kare su daga yunwa, sakaci da cin zarafi.

Jakadan Saudiyya a Najeriya, Yousef Bin Muhammed Albalawi, ya tabbatar da aniyar ƙasarsa ta ƙara bunƙasa dangantaka da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng