Ana Maganar 2027, Gwamna Ya Kirkiro Sabuwar Masarauta a Jiharsa

Ana Maganar 2027, Gwamna Ya Kirkiro Sabuwar Masarauta a Jiharsa

  • Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya amince da ƙirƙirar sabuwar gunduma a ƙaramar hukumar Suru domin ƙarfafa tsarin masarautun gargajiya
  • Haka kuma gwamnan ya ɗaga matsayin Mai Unguwar Tarasa zuwa hakimi bayan raba yankin daga gundumar Kola a ƙaramar hukumar Birnin Kebbi
  • Gwamnatin jihar ta ce matakan sun yi daidai da dokar ƙananan hukumomin jihar Kebbi ta shekarar 2008 kuma sun fara aiki nan take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Birnin KebbiGwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ya amince da ƙirƙirar sabuwar gunduma a ƙaramar hukumar Suru tare da ɗaga matsayin Mai Unguwar Tarasa zuwa hakimi a ƙaramar hukumar Birnin Kebbi.

An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu na jihar, Garba Dutsinmari, ya fitar a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya gwangwaje shugabannin makarantu da babbar kyauta

Gwamna Nasir Idris a jihar Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi yayin tattaunawa da 'yan jarida. Hoto: Nasir Idris
Source: Facebook

Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnatin ta ce an ɗauki matakin ne domin ƙarfafa tsarin shugabancin gargajiya da inganta shugabanci domin samar da rayuwa mai kyau ga al'umma.

Nade naden da aka yi a Kebbi

A cewar sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, an ƙirƙiri gundumar Zarmakwai ne daga cikin gundumar Aljannare da ke ƙaramar hukumar Suru.

Haka kuma, gwamnatin Kebbi ta bayyana cewa an naɗa Alhaji Aliyu Abubakar Sarki a matsayin hakimin farko na sabuwar gundumar Zarmakwai.

Bugu da ƙari, an ɗaga matsayin Mai Unguwar Tarasa zuwa gunduma bayan an raba yankin daga gundumar Kola da ke ƙaramar hukumar Birnin Kebbi.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin ta amince da naɗa Alhaji Faruku Abubakar a matsayin hakimin sabuwar gundumar Tarasa.

An yi nasiha ga sarakunan gargajiya

Kwamishinan ya bayyana cewa an ɗauki matakan ne bisa tanadin sashe na 10, ƙananan sashe na (A) da (B) na dokar ƙananan hukumomin jihar Kebbi ta shekarar 2008.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta lallaba Saudiyya, tana so a taimaka wa Najeriya kan karatun allo

Ya buƙaci sababbin hakiman da aka naɗa su tabbatar sun cika amanar da aka ɗaura masu ta hanyar gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, riƙon amana da sadaukarwa.

Taswirar jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Ya ƙara da cewa cibiyoyin gargajiya na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaban al'umma da kuma kyakkyawan shugabanci a matakin ƙasa.

A shekarar 2025 mai dai gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da naɗa sababbin hakimai guda tara da dagatai guda biyar kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Rahotanni da aka fitar a wancan lokacin sun nuna cewa gwamnan ya ce an dauki matakin ne saboda kara kusantar masu ruwa da tsaki ga jama'a.

An yi auren gata a Kebbi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da gudanar da shirin auren gata na jama'a kyauta a duk tsawon wa'adinsa.

Gwamnan jihar Kebbi ya bayyana haka ne yayin bikin auren mutane 300 da aka gudanar a filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi.

A bayanin da ya yi, Gwamna Nasir Idris ya ce shirin ya zama wata muhimmiyar hanyar tallafa wa iyalai marasa ƙarfi tare da rage masu nauyin kashe kuɗin aure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng