Majalisar Dattawa Ta Amince da Bukatar Tinubu, Ta Tabbatar da Nadin Sababbin Ministoci 2
- Majalisar dattawa ta amince da bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta nadin sabon ministan lantarki, Joseph Olasunkanmi Tegbe
- Hakan dai ya biyo bayan tantancewar da Majalisar ta yi wa Tegbe, awanni 24 bayan Shugaba Tinubu ya mika sunansa domin ya nada shi
- Bayan haka, sanatocin sun kuma tabbatar da kadin Ambasada Sola Enikanolaiye a matsayin karaminin ministan harkokin wajen Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Ambasada Sola Enikanolaiye a matsayin Karamin Ministan Harkokin Waje.
Haka zalika Majalisar ta amince da nadin Joseph Olasunkanmi Tegbe a matsayin Ministan Wutar Lantarki kamar yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukata.

Source: Facebook
Majalisa ta amince da nadin ministoci 2
Jaridar Punch ta ruwaito cewa amincewar ta biyo bayan tantancewar da aka yi wa wadanda aka nada a zaman majalisar dattawa, inda aka yi masu tambayoyi kafin yanke hukuncin karshe.
Tun farko, Tinubu, a wasiku daban-daban da ya aika wa majalisar a ranar Talata, ya nemi amincewarta kan nadin sababbin ministocin bisa tanadin kundin tsarin mulki.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya karanta wasikun a zauren majalisar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Daga nan aka mika batun ga kwamitin gaba daya domin duba shi cikin gaggawa, kamar yadda dokokin majalisa suka tanada.
Takaitaccen bayani kan ministocin
Tabbatar da nadin Enikanolaiye a matsayin Karamin ministan harkokin waje ya tabbatar da dawowarsa sahun gaba a harkokin diflomasiyyar Najeriya.
Dan asalin jihar Kogi, sabon ministan ya taba rike Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban kasa kan harkokin waje da dangantakar kasa da kasa, ya kuma rika babban sakataren ma'aikatar harkokin waje.
A bangaren Tegbe kuwa, nadinsa ya zo a wani lokaci mai muhimmanci ga bangaren lantarki, wanda ke fama da matsalolin karancin kudi da kayan aiki duk da gyare-gyaren da gwamnati ke yi karkashin shirin “Renewed Hope."
Dalilin nada sabon Ministan Lantarki
Nadinsa ya biyo bayan murabus din tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, wanda ya sauka a watan Maris 2026 domin shiga takarar gwamnan jihar Oyo a zaben 2027.
Tegbe, dan asalin jihar Oyo, yana da gogewa fiye da shekaru 30 a fannin manufofin tattalin arziki da gyare-gyare a bangaren gwamnati da masu zaman kansu.

Source: Instagram
Ya taba zama babban abokin hulda kuma shugaban sashen shawarwari a kamfanin KPMG Africa, kuma a yanzu shi ne Darakta Janar kuma mai kula da hulda tsakanin Najeriya da China.
Haka kuma ya jagoranci kwamitin aiwatar da manufofin haraji na kasa da aka kafa a 2025, tare da taka rawa a gyare-gyaren dokoki da cibiyoyi a bangaren lantarki.
Majalisa ta amince Tinubu ya ci bashi
A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar dattawa ta sahalewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karbo bashin Dala miliyan 516 domin gina titin Sokoto zuwa Badagry.
Hakan ya biyo bayan nazari da Majalisar dattawan ta yi kan rahoton d kwamitin kula da basussukan cikin gida da na waje ya gabatar.
Yayin muhawara, mambobin majalisar dattawan sun jaddada mahimmancin wannan aiki na titi da ya taso daga jihar Sokoto zuwa Badary da ke jihar Legas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

