Gobara: 'Yan Kasuwar Kano Sun Bi Sawun N5bn na Tallafin Tinubu

Gobara: 'Yan Kasuwar Kano Sun Bi Sawun N5bn na Tallafin Tinubu

  • Yan kasuwar Kano da iftila'in gobara ya shafa sun tunatar da gwamnatin tarayya alkawarin da ta yi na tallafa masu da kudi bayan konewar kadarorinsu
  • Wasu daga cikin yan kasuwar da su ka wakilci sauran sun yi tattaki kafa da kafa inda su ka tattauna da babba a gwamnatin Bola Tinubu
  • Gwamnatin Tarayya ta kai ziyara wurin gobarar da ta afku a farkon 2026 inda aka yi mummunar asara da ta lalata dukiyoyin biliyoyin Naira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tawagar shugabannin 'yan kasuwa da jami'an gwamnatin Kano ta gana da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume.

An yi wannan zama na musamman ne domin neman a gaggauta fitar da tallafin N5bn da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin bai wa waɗanda gobarar kasuwar Singer ta shafa.

Kara karanta wannan

Atiku ya kalubalanci Tinubu kan sayo motocin alfarma a kan N15.13bn

Yan kasuwa a Kano sun ziyarci sakataren gwamantin tarayya
Tawagar yan kasuwa da su ka ziyarci sakataren gwamnati George Akume Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

Wannan na kunshe a cikin sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature D-Tofa ya fitar kuma Ibrahim Adam, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Tawagar yan kasuwar Kano ta gana da gwamnati

Jaridar The Nation ta kawo labarin cewa tawagar ta bayyana wa Akume cewa shugaban ƙasa ya yi alƙawarin tallafa wa 'yan kasuwar da gobarar ta lalata masu shaguna da dukiyoyi a farkon shekarar nan.

Tawagar ta kara da cewa lokaci ya yi da ya kamata a cika wannan alƙawari domin farfaɗo da harkokin kasuwanci a ɗaya daga cikin manyan kasuwannin Arewacin Najeriya.

Wani mamba na tawagar ya ce:

"Muna godiya ga Mai Girma Shugaban Ƙasa saboda tunawa da al'ummarmu, amma watanni biyar bayan alƙawarin, har yanzu 'yan kasuwa da dama ba su iya sake cika shagunansu da kaya ba."

Su waye su ka zauna da gwamnati?

Tawagar ta haɗa da shugaban Ƙungiyar Al'ummar Kasuwancin Kano, Alhaji Sabiu Bako da Kwamishinan Kuɗi na Jihar Kano, Isma'il Aliyu Danmaraya.

Kara karanta wannan

NDC: 'Gwamnatin Kano ta karbo diyyar Hausawa da aka hallaka a Uromi'

Sai kuma wani jigo a APC, Muhammad Jamu Yusuf; shugaban Kasuwar Singer, Junaidu Muhammad Zakari; da ɗan kasuwa Kabiru Adamu Gano.

Tinubu ya yi alkawarin ba yan kasuwar Kano tallafin kudi bayan gobara ta afku
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Getty Images

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, an ce Sanata Akume ya saurari bukatun tawagar .

Bayan ya kammala jin bayanansu kuma ya tabbatar masu cewa an karɓi koken nasu, sannan ya yi alkawarin zai hanzarta matakan da suka dace domin a saki kuɗaɗen tallafin.

Gobara ta kama a kasuwar Kano

A baya, kun samu labarin cewa a karo na biyu cikin kasa da makonni biyu, kasuwar Singer da ke cikin jihar Kano ta sake fuskantar ibtila'in gobara ranar Asabar, 14 ga watan Fabrairu, 2026.

Rahotanni daga yan kasuwa sun nuna cewa gobarar ta kama ne a sashen Gidan Glass da wuraren 4.00 na yamma kuma an shafe lokaci ba a samu agajin da ya dace a kan lokaci da gobarar ta tashi ba.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa gobarar ta samo asali ne daga wani shagon sayar da kayan masarufi, inda aka ga hayaƙi mai kauri ya mamaye sararin samaniya tare da haddasa ruɗani a cikin kasuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng