Shirin Hajjin 2027: NAHCON Ta Fadi Miliyoyin da Alhazai Za Su Fara Ajiye wa

Shirin Hajjin 2027: NAHCON Ta Fadi Miliyoyin da Alhazai Za Su Fara Ajiye wa

  • NAHCON ta buƙaci masu niyyar Hajjin 2027 su fara biyan ajiyar Naira miliyan biyar domin tabbatar da gurabensu da sauƙaƙa shirye-shiryen tafiya
  • NAHCON ta fara karɓar ajiyar kuɗin Hajjin 2028 zuwa 2030, tana ƙarfafa maniyyata su rika tara kuɗi a hankali ta hukumomin jihohi da bankuna
  • Jihohin Kwara da Taraba sun buƙaci maniyyata su kammala biyan kuɗi da takardu kafin 26 ga Satumba, 2026, domin kauce wa matsalolin biza

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja - Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta buƙaci masu niyyar gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027 su fara ajiye kuɗi har Naira miliyan biyar domin tabbatar da gurabensu.

A cikin wata sanarwa, hukumar ta ce fara biyan kuɗin tun da wuri zai ba maniyyata damar tabbatar da samun gurbi, rage musu nauyin biyan kuɗin Hajji ta hanyar biyan kuɗi a hankali, tare da bai wa NAHCON damar shirya masauki da sauran ayyuka cikin lokaci.

Kara karanta wannan

'Ku dakatar da gina gadar sama': Tinubu ga gwamnoni, ya kawo masu mafita

Hukumar NAHCON ta bukaci maniyyatan Najeriya su fara ajiye kudin Hajjin 2027
Alhazai na gudanar da hawan Arafat a Saudiyya da kuma tambarin hukumar NAHCON.
Source: Getty Images

An fara karɓar ajiyar Hajjin 2028 zuwa 2030

Hukumar ta kuma sanar da fara karɓar ajiyar kuɗin aikin Hajji na shekarun 2028, 2029 da 2030. kamar yadda rahoton Daily Trust ya nuna.

Ta buƙaci masu sha'awar zuwa Hajji su fara tara kuɗinsu ta hannun Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jiharsu ko kuma bankunan da aka amince da su a ƙarƙashin Shirin Ajiya na Hajji (Hajj Savings Scheme).

NAHCON ta ce wannan tsari zai ba masu niyyar aikin Hajji damar rarraba kuɗin tafiyarsu cikin lokaci, yayin da hakan kuma zai taimaka wa hukumar da hukumomin jihohi wajen yin shirye-shiryen da suka dace da kuma samar da ingantattun ayyuka ga alhazai.

Kwara da Taraba sun sanya wa'adi

A wani ci gaba kuma, Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na jihohin Kwara da Taraba sun buƙaci masu niyyar aikin Hajjin 2027 su kammala biyan kuɗinsu da gabatar da takardunsu kafin ranar 26 ga Satumba, 2026.

Kara karanta wannan

Yadda aka ware N400bn na gyaran masallatai, masarautu a kasafin kudin 2026

Jaridar Punch ta rahoto cewa sun ce wannan ita ce wa'adin da NAHCON da hukumomin Saudiyya suka gindaya.

Sakataren zartarwa na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar Kwara, Abdulsalam Abdulkadir, ya ce jinkirin biyan kuɗi ko kammala takardu na iya kawo tsaiko wajen fitar da biza, lamarin da ka iya hana wasu zuwa aikin Hajjin bana.

Ya tuna cewa a shekarun baya wasu maniyyata sun rasa damar zuwa Hajji saboda rashin cika sharuɗɗa cikin lokaci, yayin da wasu kuma suka nemi a mayar musu da kuɗinsu bayan wa'adin ya wuce.

Taraba ta buƙaci a fara biyan kuɗi da wuri

Shi ma mukaddashin sakataren zartarwa na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar Taraba, Alhaji Abubakar Usman Tanko, ya ce masu niyyar aikin Hajji a jihar za su fara da biyan Naira miliyan bakwai a matsayin ajiya.

Ya ce hukumar ta shirya gudanar da wayar da kai a faɗin jihar domin sanar da maniyyata sabbin dokoki da ƙa'idojin da hukumomin Saudiyya suka gabatar.

Hukumar NAHCON ta ce maniyyata su fara ajiye N5m don fara shirin Hajjin 2027
Sugabannin hukumar gudanar da aikin Hajji ta Najeriya, watau NAHCON na taro a Abuja. Hoto: @nigeriahajjcom
Source: Twitter

Tanko ya buƙaci masu niyyar aikin Hajji su gaggauta biyan kuɗinsu domin bai wa hukumar damar cika wa'adin da aka sanya tare da kauce wa rasa damar zuwa Hajji.

Kara karanta wannan

An fadi sunayen 'yan ta'adda 5 da aka kama suna sace dalibai da aka je kotu

Ya ƙara da cewa hukumar ta Taraba na ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da an gudanar da aikin Hajji ba tare da wata matsala ba.

A cewarsa, alhazai 714 daga jihar Taraba sun gudanar da aikin Hajjin 2026 cikin nasara, sai dai mutum ɗaya ya rasu, yayin da wani kuma ya rasa hannu sakamakon haɗarin mota kafin tafiya zuwa ƙasa mai tsarki.

Musulman da suka je Hajjin 2026

A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar ƙididdiga ta Saudiyya ta sanar da cewa mahajjata miliyan 1.7 ne suka gudanar da aikin Hajjin 2026, adadin da ya zarce na 2025.

Mahajjata daga sassa daban-daban na duniya sun gudanar da ibadu a Arafah, Muzdalifah da Mina cikin tsauraran matakan tsaro.

Wasu mahajjata sun bayyana aikin Hajjin a matsayin aikin da ake yi cikin tsananin zafi, amma mai cike da shauki na samun kusanci da Allah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com