Gwamnati Za Ta ba Ma'aikata Hutun Kwanaki 9 domin Bukukuwan Sallar Layya a Turkiyya
- Shugaba Recep Erdoğan ya ba da sanarwar ƙara hutun Sallar Layya na shekarar 2026 zuwa kwanaki tara ga ma'aikatan gwamnati a Turkiyya
- Bukukuwan sallar za su fada tsakanin 27 zuwa 30 ga watan Mayu, inda aka haɗe kwanakin aiki na Litinin da Talata don samun hutu mai tsawo
- Legit Hausa ta tattaro bayanai game da yadda ake gudanar da bukukuwan sallah a kasar Montenegro da wasu daga cikin garuruwan Turkiyya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Turkiyya - A ranar Litinin, Shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya sanar da cewa hutun sallar layya (Qurban Bayram) mai zuwa zai kai kwanaki tara ga ma'aikatan gwamnati, domin samar da dogon hutu a lokacin bikin.
Da yake jawabi bayan taron Majalisar Ministoci a fadar shugaban ƙasa da ke Ankara, Erdoğan ya ce shawarar ta haɗa da ƙarin hutun gudanarwa domin tsawaita lokacin hutun a hukumance.

Source: Getty Images
An tsawaita hutun bikin sallah a Turkiyya
Sallar Layya za ta gudana ne daga ranar 27 zuwa 30 ga watan Mayu, kamar yadda rahoton jaridar Turkiye Today ya nuna.
A ƙarƙashin sabon tsarin, ma'aikata za su fara hutunsu ne daga ranar Talata, 26 ga watan Mayu da rana, inda aka ba su ƙarin kwana ɗaya da yini na hutun kafin ranar Idi.
Shugaban ya bayyana cewa:
"Ta hanyar haɗa kwana ɗaya da rabi kafin Idin a matsayin hutun gudanarwa, mun samar da jimillar kwanaki tara na hutu ga ma'aikata."
Wannan matakin ya mayar da ranar Litinin, 25 ga watan Mayu, da safiyar Talata, 26 ga watan Mayu, waɗanda asali kwanakin aiki ne, zuwa ranakun hutu.
Al’adun Sallar Layya a tsakanin Musulmin Balkan
Sallar layya, wadda Turkawa ke kira da Kurban Bayram, tana ɗaya daga cikin manyan bukukuwan Musulunci da ake gudanarwa don tunawa da sadaukarwar Annabi Ibrahim (AS), in ji rahoton Daily Sabah.
Musulmi na gudanar da bukukuwan ne ta hanyar sallah, walima, da ayyukan jinƙai. Legit Hausa ta tattaro yadda ake gudanar da bukukuwan babbar sallah a wasu biranen Turkiyya.
- Balkan: A yankin Balkan, inda aka samu cakuduwar al'adu daban-daban, sallar layya tana ɗaukar sabon salo mai kayatarwa.
- Montenegro: Musulmi na gudanar da biki cikin nishaɗi, inda ake rarraba naman layya ga dangi da mabukata don nuna jin kai ga juna.
- Bulgaria: Turkawa da Pomak na gudanar da bikin sallar tare, inda yara ke ziyartar manya don karɓar kyaututtuka, alawa, da kuma samun albarka.
- Bosnia da Herzegovina: Ana gudanar da sallar Idi a masallatai masu tarihi kamar Gazi Husrev-beg da ke Sarajevo, tare da cin abinci na gargajiya kamar Borek da Baklava.
- Slovenia: Ko da yake Musulmi tsiraru ne a Slovenia, suna gudanar da layya tare da nuna haɗin kai mai ƙarfi tsakanin mabiya addinin.

Source: Getty Images
Wannan babban hutu na kwanaki tara da aka bayar a Turkiyya zai ba wa ma'aikata damar gudanar da waɗannan al'adu na yin layya, ziyarar dangi da kuma yawon buɗe ido cikin kwanciyar hankali, duba da cewa wannan biki ne na karfafa zumunta.
UAE: An kayyade farashin dabbobin layya
A wani labari, mun ruwaito cewa, Dubai ta amince da ƙayyadadden farashin dabbobin layya na shekarar 2026 domin kauce wa tsadar da ba ta dace ba.
Farashin dabbobin ya fara ne daga Dirham 350 zuwa Dirham 800, ya danganta da nau'in dabba da kuma inda za a gudanar da yanka da rarrabawa.
Ana sa ran gudanar da sallar layya ta shekarar 2026 a ranar 27 ko 28 ga watan Mayu, ya danganta da ranar da aka ga jinjirin watan Zul Hijjah.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


