‘Mahaddacin Kur’ani ne’: An Fadi Riko da Addini na Babban Soja da Aka Kashe

‘Mahaddacin Kur’ani ne’: An Fadi Riko da Addini na Babban Soja da Aka Kashe

  • Masu amfani da kafofin sadarwa sun bayyana rasuwar Kanal Abdulsalam Ude na DIA a Abuja a matsayin babban rashi
  • Uthman Isa Tochukwu ya ce marigayin ya haddace Alkur'ani gaba ɗaya, ya kware a harshen Larabci, kuma yana cikin jami'an leken asiri
  • Masu alhini sun ce rasuwarsa babban rashi ne ga Musulman Igbo da Najeriya baki ɗaya, tare da yi masa addu'ar Allah Ya gafarta masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wasu rahotanni sun bayyana yadda babban soja da yan bindiga suka hallaka ke da riko da addini.

An tabbatar da cewa maharan sun kashe Kanal Abdussalam Ude na rundunar sojojin Najeriya a gidansa da ke kusa da Abuja.

An yaba wa riko da addini na babban soja da aka hallaka
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Wani mai amfani da shafin X, Uthman Isa Tochukwu ya yi jimamin mutuwar babban sojan inda ya ce Musulunci ya yi rashi.

Kara karanta wannan

Sardaunan Sokoto, Abubakar Alhaji ya riga mu gidan gaskiya

Yadda mutuwar babban soja ta girgiza Musulmai

Mutane sun ci gaba da bayyana alhininsu kan rasuwar Kanal Abdulsalam Ude na Hukumar Leken Asirin Tsaro ta Kasa (DIA), wanda aka kashe bayan rahotanni sun ce ya yi yunkurin hana masu garkuwa da mutane sace shi a gidansa da ke Abuja.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne jim kadan bayan marigayin ya isa gidansa da ke Phase 5 na Army Housing Estate a Kurudu, kusa da Abuja, da misalin karfe 10:45 na daren Litinin.

Uthman Isa Tochukwu ya ce rasuwar Kanal Ude ta yi matukar girgiza al'ummar Musulman Igbo, yana mai bayyana cewa marigayin ya haddace Alkur'ani mai girma gaba daya.

Tochukwu ya kara da cewa Kanal Ude ya kasance kwararre a harshen Larabci, inda ya ce kwarewarsa ta kai matsayin da ake ganin ya fi wasu Larabawa iya amfani da harshen.

Ya kuma bayyana marigayin a matsayin gogaggen jami'in leken asirin soja, yana mai cewa yana cikin fitattun kwararrun jami'an tsaro da Najeriya ke da su a halin yanzu.

Kara karanta wannan

An daure dalibin Jami'ar Jos, an masa duka da katako sai da ya mutu kan waya

A cewarsa, ana sa ran za a kara wa Kanal Ude girma zuwa mukamin Birgediya Janar a shekara mai zuwa, mukamin da ya ce babu wani Musulmin Igbo da ya taba kaiwa a rundunar sojin Najeriya.

An bayyana rikon addini da marigayi tsohon soja ke da shi
Marigayi Kanal Abdussalam Ude da yan bindiga suka hallaka. Hoto: @UthmanTochukwu.
Source: Twitter

Lambobin yabo da marigayin ya samu

Tochukwu ya ce marigayin ya samu lambobin yabo da dama saboda bajintarsa a fannin leken asiri da tsaro, sannan ya kasance mutum mai natsuwa da nutsuwa wajen mu'amala.

Ya ce Kanal Ude malamin Alkur'ani ne kuma jagora ga matasa da dama, yana mai cewa zai dauki lokaci mai tsawo kafin a samu irinsa a cikin al'umma.

Ya ce:

“Ga waɗanda ba su san marigayi Kanar AA Ude ba, da kuma dalilin da ya sa mutuwarsa mai cike da ruɗani ta yi mana zafi ƙwarai (mu Musulman Igbo).
“Sheikh Kanar AA Ude ya kasance Hafizul Alƙur’ani, wato ya haddace Alƙur'ani mai girma gaba ɗaya.
“Ya kasance ƙwararre a harshen Larabci; yana iya magana da harshen cikin ƙwarewa, har wasu na ganin ya fi wasu Larabawa iya amfani da shi.”

Yan bindiga sun kashe tsohon soja

A wani labarin, an ji cewa yan bindiga sun kashe tsohon soja a Nasarawa A baya, mun ba ku labarin cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari wata unguwa da ke kan iyakar Abuja da Nasarawa, inda suka sace wata mata da tsakar dare.

Kara karanta wannan

Yadda aka shirya amfani da Boko Haram, JTF domin kifar da gwamnatin Tinubu

Wani tsohon sojan Najeriya ya fito domin taimakawa lokacin harin, amma maharan sun harbe shi har ya mutu nan take lamarin da ya tayar wa jama'ar yankin hankali.

Rundunar ƴan sanda ta fara bincike, yayin da jami'an tsaro suka ƙara ƙaimi domin ceto matar da aka sace tare da kamo waɗanda suka kai harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.