Latest
Bankin EBID na ECOWAS ya bai wa gwamnatin jihar Bauchi rancen dala miliyan 91.63 domin gina tituna da gadoji 24, tare da samar da dubban guraben aiki.
Fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara ya ce bai ambaci sunan kowa a sabuwar wakarsa ba, yana mai cewa duk wanda ya tsargu ya dauki maganar da kansa.
Wasu shugabannin kabilar Igbo sun goyi bayan alkawarin Peter Obi na wa’adi ɗaya, yayin da wasu ke ganin yarjejeniyar ba ta amfani Kudu maso Gabas.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ba da umarnin rusa haramttun Rugage a Kukwaba, yana cewa ta zama mafakar masu laifi kuma barazana ga tsaron Abuja.
Rundunar sojin Najeriya ta ceto Laftanar Kanar Ofor Amobi da wani farar hula bayan kwanaki 10 ana samame a dazukan Enugu, yayin da masu garkuwa suka tsere.
John Cardinal Onaiyekan ya ce Bola Tinubu ya bayyana wa bishops na Cocin Katolika karara cewa bai amince da ra'ayinsu kan tattalin arziki da tsaron Najeriya ba.
INEC ta ce ba ta amince da takarar Goodluck Jonathan da bangaren Kabiru Turaki na PDP ya mika ba, yayin da bangaren ya dage cewa ya bi doka wajen mika sunayen.
Peter Obi ya ce da shi ne shugaban kasa, da kansa zai shiga dajin da aka boye dalibai da malamai da aka sace a Oyo, tare da sukar yadda ake tafiyar da tsaro.
ADC ta bukaci Bola Tinubu ya yi amfani da dabarar da ta kai ga ceto mutanen Oriire a Oyo wajen kubutar da sauran mutanen da aka sace a fadin Najeriya.
Masu zafi
Samu kari