APC Ta Fara Zare Ido ga Wasu na Kusa da Tinubu game da Zaben 2027

APC Ta Fara Zare Ido ga Wasu na Kusa da Tinubu game da Zaben 2027

  • Jam'iyyar APC ta yi gargadi ga wasu mukarraban Bola Tinubu yayin da ake shirin zaben 2027 da ake tunkara a Najeriya
  • Shugaban APC Nentawe Yilwatda ya ce masu mukaman siyasa ba za su kira kansu ƙwararru kawai ba tare da taka rawar siyasa a mazabunsu ba
  • Shugabannin kananan hukumomi sun ce suna da goyon bayan shugabanni da dama, tare da burin tabbatar APC ta samu akalla kashi 70 na kuri'un 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam'iyyar APC ta yi gargadi duk masu mukaman siyasa da ke aiki a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu game da yi masa kamfen.

APC ta ce dole su taimaka wajen yakin neman kuri'un jam'iyya ko kuma su bar mukamansu nan take.

APC ta gargadi masu mukamai a mulkin Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da shugaban APC, Nentawe Yilwatda. Hoto: All Progressives Congress.
Source: Twitter

Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana hakan a Abuja lokacin da ya karbi shugabannin dandalin shugabannin kananan hukumomi na jam'iyyar APC, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

APM ta ce Tinubu ya tara malaman addini ya sharara masu karya

APC ta tuna muhimmancin ciyamomi a Najeriya

Ya ce shugabannin kananan hukumomi sun fi sanin halin da masu mukaman gwamnati suke ciki saboda suna kusa da jama'a fiye da jami'an gwamnati da ke Abuja.

Yilwatda ya ce shugabannin kananan hukumomi ne za su iya bayyana ko kwamishina ko babban jami'i yana aiki a ofis amma ba ya taimakawa jam'iyya a mazabarsa.

Ya ce duk wanda aka ba mukamin siyasa ba zai iya cewa shi ba ɗan siyasa ba ne, domin mukamin da yake rike da shi ya samo asali ne daga siyasa.

A cewarsa, duk wanda ba ya son shiga harkokin siyasa ya kamata kada ya karɓi mukamin siyasa, domin nasarar gwamnati tana dogara ne da kuri'un jama'a.

An gargadi masu makamai kan tallata Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya a taro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Alkawarin da shugaban APC ya yi

Shugaban APC ya yi alkawarin mara wa dandalin shugabannin kananan hukumomi baya domin ƙarfafa aikin wayar da kan masu kada kuri'a da kuma samun nasara a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

ADC ta kalubalanci Tinubu ya ziyarci Zamfara bayan mummunan hari

Tun da farko, shugaban dandalin, Dakta Mustafa Jibrin, ya ce suna da goyon bayan shugabannin kananan hukumomi 685 da gwamnoni 31, tare da burin APC ta samu akalla kashi 70 na kuri'un zaɓen 2027.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da babban zaben shekarar 2027 da ake ganin zai yi matukar zafi a Najeriya, cewar Punch.

Ana ci gaba da sukar salon mulkin Tinubu yayin da ake tunkarar zaben duba da irin rashin tsaro da ya yi kamari da kuma matsin tattalin arzikin Najeriya.

Wanda ya tallafa Tinubu ya sha duka

Mun ba ku labarin cewa gwamnatin jihar Delta ta umarci jami'an tsaro su gano tare da kama mutanen da suka kai hari kan Simon Mudi, hadimin gwamna Sheriff Oborevwori.

An kai harin ne yayin taron masu ruwa da tsaki na APC a Delta ta Tsakiya, inda aka ji wa Simon Mudi da wasu raunuka masu tsanani.

Tsohon minista Solomon Dalung ya ce Simon Mudi na ci gaba da samun sauki, yana kuma godiya ga 'yan Najeriya da suka yi masa addu'a da nuna goyon baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.