DSS, Dakarun Daji Sun Gwabza Ƙazamin Faɗa da Ƴan Bindiga a Kwara, An Rasa Rayuka

DSS, Dakarun Daji Sun Gwabza Ƙazamin Faɗa da Ƴan Bindiga a Kwara, An Rasa Rayuka

  • Jami’an DSS, dakarun daji, mafarauta da ‘yan banga sun yi artabu da ‘yan bindiga a dajin Kwara, inda suka kashe uku tare da ceto mutum tara
  • Wadanda aka ceto sun hada da manoma da aka sace daga gonaki da kuma wasu da aka yi garkuwa da su daga jihar Ekiti kafin a kubutar da su
  • Hukumar tsaron da ta gudanar da samamen ta ce har yanzu ana bukatar karin kayan aiki domin karfafa yaki da masu garkuwa da mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Kwara - Jami’an hukumar DSS tare da hadin gwiwar dakarun daji na jihar Kwara, mafarauta da ‘yan banga sun ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su.

Sun samu wannan nasarar ne bayan sun kashe wasu ‘yan bindiga uku a wani samame da aka kai a ƙaramar hukumar Ekiti ta jihar Kwara.

Kara karanta wannan

An kama matashi da buhunan abinci da wasu muhimman kaya zai kai wa Boko Haram

DSS da sauran jami'an tsaro sun ceto mutanen da aka sace a Kwara
Jami'an hukumar DSS a bakin aiki. Hoto: @OfficialDSSNG
Source: Facebook

Fadan jami'an tsaro da 'yan bindiga

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa wadanda aka ceto sun hada da manoma da aka sace daga gonakinsu da kuma wasu mutanen da aka yi garkuwa da su tun farko a jihar Ekiti.

Sun samu ‘yanci ne bayan masu garkuwar sun tsere sakamakon musayar wuta mai zafi da jami’an tsaro.

An gudanar da aikin ne a yankunan Obbo Aiyegunle, Ejiu Ora da Osi, da ke iyaka da jihohin Ekiti da Neja.

Mai magana da yawun shugaban ƙaramar hukumar Ekiti, Prince Dada Sunday, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa bayanan sirri da jami’an tsaro suka tattara ne suka taimaka wajen kai samamen.

A cewarsa, sama da mutum goma daga cikin masu garkuwar sun tattara wadanda suka sace daga wurare daban-daban kafin jami’an tsaro suka kai farmaki.

Mutum daya ya samu munanan raunuka

Sunday ya ce daya daga cikin wadanda aka sace ya samu mummunar sara a kai bayan ya yi yunkurin hana masu garkuwar dauke shi.

Kara karanta wannan

Sakon da Tinubu ya aika Kaduna bayan umarnin a farauto 'yan bindiga

Ya kara da cewa dukkan mutum tara da aka ceto sun samu ‘yanci ne a wurin artabun, yayin da ‘yan bindiga uku suka mutu, sauran kuma suka tsere cikin daji da raunukan harbin bindiga.

Daya daga cikin wadanda aka kubutar, Umaru Mu’azu daga Obbo Aiyegunle, ya ce masu garkuwar sun bayyana ba zato ba tsammani suka yi musu barazana da bindiga.

A nasa bangaren, wani manomi da aka ceto, Ibrahim Danga, ya ce suna hannun masu garkuwa ne kafin jami’an tsaro suka iso suka yi musayar wuta.

An bukaci karin kayan aiki

Wani jami’in dakarun daji na jihar Kwara, Owolabi Adebayo, ya bayyana cewa aikin ya samu nasara ne bisa bayanan sirri.

DSS, dakarun daji sun gwaza fada da 'yan bindiga a Kwara
Taswirar jihar Kwara, inda jami'an tsaro suka fafata da 'yan bindiga. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce sun kwato wadanda aka sace tare da kashe uku daga cikin ‘yan bindigar, amma ya jaddada bukatar samar da karin kayan aiki irin su rigunan kariya, na’urorin hangen dare, walkie-talkie da karin harsasai domin kara inganta ayyukan tsaro.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kwara, Ojo Adekimi, ya bayyana cewa DSS ce ke jagorantar ayyukan Forest Guards a jihar.

Samamen na baya-bayan nan ya biyo bayan wasu hare-haren da jami’an tsaro suka kai kan masu garkuwa da mutane a Kwara, inda a makonnin baya suka kashe wasu ‘yan bindiga biyu tare da ceto wasu yara biyu da aka sace.

Kara karanta wannan

An samu sababbin bayanai kan yadda aka sace shugaban karamar hukuma a Zamfara

Jami'an tsaro sun fafata da 'yan bindiga

A wani labari, mun ruwaito cewa, Jami'an tsaro hadin gwiwa sun samu nasarar kashe 'yan bindiga da dama yayin da aka dakile hari a kauyen Guga da ke jihar Katsina.

Rahotanni sun ce fiye da 'yan bindiga 200 ne suka yi zuga wajen kai harin ƙarƙashin jagorancin kasurgumin dan ta'adda, Idi Abasu Aiki.

Gwamnatin Katsina ta tabbatar da mutuwar mafarauta biyar tare da yabawa sadaukarwarsu wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com