Yaki da Yunwa: Oluremi Ta Fadi Yadda Tinubu Zai Tallafa wa 'Yan Kasa da Abinci

Yaki da Yunwa: Oluremi Ta Fadi Yadda Tinubu Zai Tallafa wa 'Yan Kasa da Abinci

  • Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta ce gwamnatin tarayya za ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da yunwa da ƙarancin abinci mai gina jiki
  • Ta bayyana cewa shirin rarraba kayan abinci da bankunan abinci na al'umma na tallafa wa masu buƙata, nakasassu da yara
  • Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yaba da shirin, yana mai cewa Ondo ta amince da takarar Bola Tinubu a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Akure, Ondo - Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kyautatawa al'umma.

Oluremi ta ce gwamnati tana kokari domin ƙarfafa matakan yaƙi da yunwa da ƙarancin abinci mai gina jiki ga yara.

Oluremi ta yaba salon mulkin Bola Tinubu
Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Ta bayyana hakan ne ranar Talata a Akure, babban birnin Ondo, yayin rabon kayan abinci ga marasa galihu ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiative (RHI), cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa na neman hada Obi fada da ƙabilarsa, ta fadi yadda zai cutar da su

Oluremi ta fadi yadda aka tallafa wa talakawa

Matar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Hajiya Nana Shettima, ta wakilce ta, inda ta ce shirin yana nuna jajircewar RHI wajen tallafa wa masu rauni.

Ta ce manufar shirin ita ce tabbatar da cewa yara suna samun damar girma cikin koshin lafiya, tare da ba iyalansu tallafin da suke buƙata.

Oluremi Tinubu ta ce shirin RHI yana cika manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hanyar taimaka wa 'yan Najeriya.

Ta bayyana cewa shirin rarraba kayan abinci ya fara ne tun watan Maris na shekarar 2024 domin tallafa wa nakasassu da sauran marasa galihu.

Ta jaddada cewa:

"Babu wani ɗan Najeriya da ya kamata ya kwana da yunwa. Wannan shi ne aikinmu kuma yana cikin hangen nesan shirin Renewed Hope Initiative."

A cewarta, masu ba da gudummawa biyu ne ke samar da manyan motocin kayan abinci guda biyu a kowane wata, wanda ke ba jihohi biyu damar cin gajiyar shirin.

Kara karanta wannan

An daura auren gata ga mutum 300 a Kebbi, gwamnati za ta cigaba da shirin

Oluremi ya fadi yaddaTinubu zai kawo karshen yunwa
Shugaba Bola Tinubu da mai dakinsa, Oluremi Tinubu. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Facebook

Martanin Gwamna Aiyedatiwa kan tallafin Tinubu

A jawabinsa, gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ce wannan tallafi shaida ce ta ƙudirin gwamnatin tarayya wajen rage talauci da taimaka wa marasa galihu.

Ya ƙara da cewa shirin ya wuce rabon abinci kawai, domin yana nuna tausayi, haɗin kai da ƙoƙarin inganta rayuwar masu ƙaramin ƙarfi, cewar The Guardian.

Gwamnan ya yaba wa shirin Renewed Hope Initiative saboda hangen nesansa da ƙoƙarin gano matsalolin al'umma tare da nemo hanyoyin magance su.

Aiyedatiwa ya kuma sake jaddada goyon bayan gwamnatinsa ga Shugaba Bola Tinubu, yana cewa tuni Ondo ta amince da takararsa a zaɓen 2027.

Ya ce samar da wadataccen abinci na da matuƙar muhimmanci ga mutunci da zaman lafiyar al'umma, domin yana taimaka wa yara su fi mayar da hankali wajen karatu.

Gwamnan ya kuma buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin su ɗauki shirin a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gina al'umma mai ƙarfi ta hanyar saka hannun jari a jin daɗin jama'a.

Kara karanta wannan

'Yan APC sun yi wa Peter Obi rubdugu da ya tabo Bola Tinubu

Oluremi ta yi alkawari kan tazarcen Tinubu

An ji cewa Oluremi Tinubu ta ce za ta sanya zannuwan Akwete idan mijinta, Shugaba Bola Tinubu, ya samu wa’adi na biyu.

Uwargidan Shugaban Ƙasa ta sanar da bayar da gudunmawar Naira biliyan biyu domin farfaɗo da masana’antar saka atamfar Akwete.

Ta bukaci ’yan Najeriya su rungumi kayan gargajiya da aka kera a gida domin tallafa wa masu sana’ar saka zane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.