Tashin hankali: An kashe mutane 100, an raba mutum 98,000 da gidajensu a Taraba
- Jihar Taraba da ke yankin Arewa maso Gabas na Najeriya na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar rashin tsaro sakamakon hare-haren da ake kai wa
- Cocin Katolika ta Wukari ta fitar da alkaluma wadanda suka nuna barnar da aka tafka a wasu kananan hukumomin jihar saboda matsalar rashin tsaro
- Ta yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran hukumomin da suka dace da su tashi tsaye dlmin ceto mutanen da rikice-rikicen suka ritsa da su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Taraba - Cocin darikar Katolika ta Wukari da ke jihar Taraba, ta koka kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Ta bayyana cewa mutane 98,000 ne suka rasa matsugunansu, sannan an lalata majami’u 217 sakamakon hare-haren da ke ci gaba da faruwa a jihar.

Source: Twitter
Jaridar Premium Times ta ce Cocin Katolikan ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ƙarshen babban taronta na uku da aka gudanar ranar Asabar, 9 ga watan Mayun 2026 a Wukari.
An raba mutane da matsugunansu a Taraba
Bishop Mark Nzukwein na cocin Katolikan ne ya sanya wa sanarwar hannu.
Sanarwar ta bayyana cewa mutanen da suka rasa matsugunansu sun bazu ne musamman a kewayen ƙananan hukumomin Donga da Takum.
“Tun daga watan Satumban 2025, an samu sake ɓarkewar hare-hare daga masu aikata laifuffuka a kan al’ummomi a yankin Kudancin Taraba, musamman a ƙananan hukumomin Takum, Donga da kuma yankin raya ƙasa na musamman na Yangtu."
“Waɗannan hare-hare sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, wasu sun nakasa yayin da wasu suka ji rauni, sannan an lalata dukiyoyi na miliyoyin nairori da hanyoyin samun abinci."
“Bayanai sun nuna cewa mutane sama da 98,000 ne suka rasa matsugunansu, ciki har da limaman coci 16, yayin da aka ruguje majami’u 217 gaba ɗaya."
“An kuma lalata gidajen limaman coci takwas, sannan an bayar da rahoton kashe mutane sama da 100."
- Mark Nzukwein

Source: Original
Cocin Katolika ta koka
Cocon ta kuma koka game da yawaitar ƙwace filaye, tana mai jaddada cewa masu aikata laifuka sun ƙwace filayen kaka da kakanni na mutanen da suka rasa matsugunansu.
Sanarwar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su kasance masu taka tsantsan wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da ke addabar yankin.
Bugu da ƙari, ta yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da ta samar da matakan da za su bai wa mutanen da suka rasa matsugunansu damar komawa gidajensu.
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi wa wasu 'yan ta'dda dauke da makamai kwanton bauna a jihar Katsina.
Dakarun sojojin sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda guda uku tare da ƙwato makamai da wasu kayayyaki a hannunsu.
Sojojin sun mamaye wasu muhimman wurare a kan hanyar Turare–Kitibawa–Kuka Mai Damusa biyo bayan bayanan sirri da aka samu kan motsin wasu ’yan ta’adda da ke tserewa daga yankin Matazu.
Asali: Legit.ng

