NDC: 'Gwamnatin Kano ta Karbo Diyyar Hausawa da aka Hallaka a Uromi'
- Jam'iyyar NDC ta zargi gwamnatin Kano da karɓar diyyar Hausawa da aka yi wa kisan gilla a Uromi da ke jihar Edo
- Jam'iyyar ta ce tana da hujjoji masu ƙarfi kan zargin da ta ke yi na cewa gwamnatin Kano ta hana kudin
- Ta kuma yi zargin cewa akwai wasu kudin da aka tarana tallafawa wadanda iftila'i ya shafa a Kano, amma shiru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam'iyyar NDC ta yi zargin cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta karɓi diyyar mutanen da aka kashe a Uromi da ke jihar Edo.
A hira da Legit, Hon. Yusuf Fasaha Majidadi, mai magana da yawun NDC reshen jihar Kano, ya ce suna da hujjoji masu ƙarfi da ke tabbatar da hakan.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito yadda aka hallaka Hausawa da ke kan hanyarsu ta dawowa Arewa, inda wasu jama'a suka yi musu kisan gilla a Uromi.
Zargin NDC kan gwamnatin Kano
Kafin wannan lokaci, jaridar Vanguard ta wallafa cewa gwamnatin jihar Edo ta bayyana cewa za ta biya diyyar mutanen da aka kashe a jihar.
A hirarsa da Legit, Hon. Yusuf Fasaha ya ce:
"Abin da ke faruwa a bayyane shi ne wannan gwamnan Edo, akwai raɗe-raɗin da ke tabbatar da cewa ya biya kuɗin diyya na waɗannan mutanen da aka kashe, ƴan asalin jihar Kano daga Bunkure."
"Amma har yanzu gwamnatin jihar Kano ta yi shiru, ba ta ba su hakkinsu ba."
"Babu wata magana ma da ke cewa za a biya su kuɗin nan."
Sauran zarge-zargen NDC kan Abba
Hon. Yusuf Fasaha Majidadi ya ƙara da cewa, baya ga wannan batu, suna zargin gwamnatin Abba da hana isar da tallafin da aka bayar domin tallafa wa waɗanda gobarar Kasuwar Kantin Kwari ta shafa.

Source: Facebook
Ya ce:
"Haƙƙin mutane an ba ta ta kai musu, amma ta kasa bayarwa."
Ya kuma ƙara da cewa suna sane da ƙorafe-ƙorafen iyayen yaran da aka kashe a lokacin murnar naɗa mataimakin gwamna, Murtala Sule Garo.
Ya ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba, kuma za su ci gaba da sanya ido kan yadda ake gudanar da haƙƙin mutanen Kano tare da tabbatar da cewa an yi abin da ya dace.
Abba ya magantu kisan Uromi
A baya, mun kawo labarin cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa Bola Tinubu da gwamnan Edo kan gaggawar shiga tsakani kan kisan Hausawa .
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci a gurfanar da wadanda ake zargi a fili domin tabbatar da adalci ga iyalan da abin ya shafa da kuma bin hakkin wadanda aka kashe.
An yaba da kokarin gwamnatin Edo wajen tuntubar al’ummar Hausa da kuma alkawarin bayar da diyya ba tare da jinkiri ba ko hakan zai rage radadin da aka ji.
Asali: Legit.ng

