Yakin Iran da Amurka Ya Taba Najeriya, Farashin Kwaroron Roba Ya Tashi Sama
- Yakin da ake yi tsakanin Amurka da Iran ya shafi fannoni da dama ciki har da samar da kwaroron roba da ake amfani da shi
- Masana a fannin kiwon lafiga sun nuna fargabar cewa za a iya samun karancinsa a Najeriya sakamakon tsadar da ya yi
- Yakin da ake yi din dai ya haifar da tsadar kayayyakin da ake amfani da wasu wajen samar da kwaroron roba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida
FCT, Abuja - Masana a fannin kiwon lafiya sun yi gargaɗin cewa farashin kwaroron roba na iya tashi a Najeriya.
Sun bayyana cewa hakan na iya haifar da ƙarancinsa idan har rikicin Gabas Ta Tsakiya da ke dagula hanyoyin samar da man fetur a duniya ya ci gaba.

Source: Getty Images
Jaridar The Punch ta ce masana a fannin harhaɗa magunguna sun bayyana cewa rikicin da ke faruwa tsakanin Amurka da Iran ya haddasa tsadar kwaroron roba.
Yakin Iran da Amurka ya shafi samar da kwaroron roba
Sun bayyana cewa tuni yakin ya fara shafar samar da kayayyaki da abubuwan da ake amfani da su wajen samar da kwaroron roba, wanda hakan ke sanya kuɗaɗen kera su yin tsada.
Sun lura cewa tun da yawancin kwaroron roba da ake amfani da su a Najeriya shigowa da su ake yi daga ƙasashen waje, matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu na iya haifar da tashin farashin kwaroron roba a cikin gida, har ma da yiwuwar ƙarancinsa.
Kera kwaroron roba ya dogara ne kacokan kan sinadarai kamar roba, man sanya santsi na silicone, da sauran abubuwa, waɗanda da dama daga cikinsu sun yi tsada sakamakon tashin farashin mai da kuma matsalolin sufurin jiragen ruwa saboda yaƙin.
Za a kara farashin kwaroron roba
Masanan sun nuna wannan damuwar ne biyo bayan sanarwar da babban kamfani mafi girma a duniya wajen kera kwaroron roba, Karex, ya yi kwanan nan, inda ya bayyana shirin ƙara farashinsa da kaso 30 cikin 100 ko fiye idan har yaƙin Amurka da Iran ya ci gaba da kawo cikas wajen samar da kayayyakin kera kwaroron roba.
Kamfanin Karex, wanda ke ƙasar Malasia, yana samar wa manyan kamfanonin duniya kwaroron roba kamar su Durex da Trojan, kuma yana kera fiye da kwaroron roba biliyan biyar a shekara.
Karex ya dogara ne kan albarkatun da ake samu daga mai, ciki har da sinadarin ammonia, wanda ake amfani da shi wajen kiyaye robar latex, da kuma man sanya santsi na silicone.

Source: Getty Images
Najeriya na iya fuskantar matsala
Sai dai, masanan sun yi gargaɗin cewa ƙasashen da suka dogara da shigo da magungunan hana ɗaukar ciki daga ƙasashen waje, ciki har da Najeriya, na iya fuskantar matsalar samun su da kuma tsadar farashi idan har matsalolin suka ci gaba.
Shugaban ƙungiyar Masu Haɗa Magunguna ta Najeriya, Ambrose Ezeh, ya ce ƙaranci da kuma cikas a wajen kera kwaroron roba na iya haifar da tashin farashinsa.
An rabawa ma'aikata kwaroron roba
A wani labarin kuma, kun ji cewa an raba ma'aikata a jihar Osun kyautar kwaroron roba a ranar masoya ta duniya.
Mahalarta taron da aka yi a sakatariyar gidan gwamnatin Osun sun yi gasar rawa da wasu wasanni daban-daban kuma an bai wa zakarun kyaututuka.
Ma’aikatan, wadanda suka nuna himma a lokacin da aka raba kayayyakin, sun samu kwaroron roba na maza da mata.
Asali: Legit.ng

