An Zo Wajen: Putin Ya Yi Maganar Lokacin Kawo Karshen Yakin Rasha da Ukraine
- Ana ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun sojojin Rasha da Ukraine bayan fiye da shekaru hudu ana gwabza fada
- Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya yi tsokaci kan lokacin da za a kawo karshen yakin wanda ya jawo asarar rayuka masu yawa
- Hazalika, Putin ya nuna cewa ya shirye yake ya gana da shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy domin tattaunawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Moscow, Rasha - Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana cewa yaƙin da ƙasarsa take yi da Ukraine na iya "zuwa ƙarshe".
Putin ya nuna a shirye yake don ganawa da takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, a wata ƙasa ta daban idan har an kammala yarjejeniyar zaman lafiya.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta ce Putin ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 9 ga watan Mayun 2026 sa’o’i kaɗan bayan ya yi alƙawarin samun nasara a Ukraine yayin faretin ranar nasara na Rasha wanda aka rage girmansa fiye da na shekarun baya.
Putin ya yi ikirarin samun nasara kan Ukraine
Waɗannan kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha da Ukraine suka fara tsagaita wuta na kwanaki uku tare da amincewa su yi musayar fursunoni 1,000, cigaban da ya haifar da kyakkyawan zato na samun cigaba ta hanyar diflomasiyya.
A wajen faretin, Putin ya yaba wa dakarun Rasha da ke yaƙi a Ukraine, inda ya siffanta aikinsu a matsayin abin da ya dace da nufin yaƙar Ukraine wadda NATO ke marawa baya.
"A ko da yaushe nasara tamu ce, kuma za ta ci gaba da kasancewa tamu," in ji shi, yayin da jerin gwanon dakarun sooji suka jera a dandalin Red Square na birnin Moscow.
Me ya ce kan kawo karshen yakin?
Da yake magana da manema labarai bayan faretin, Putin ya ɗora laifin yaƙin kan "mashahuran duniya" na yammacin duniya, yana mai cewa sun yi alƙawarin cewa NATO ba za ta faɗaɗa zuwa gabas ba bayan rushewar Berlin Wall a shekarar 1989, amma daga baya suka yi ƙoƙarin janyo Ukraine cikin ƙungiyar Tarayyar Turai.

Kara karanta wannan
Alkawarin da sabon ministan makamashi ya dauka kan faduwar turakun wutar lantarki
Daga nan ya bayyana cewa:
"Ina jin lamarin yana zuwa ƙarshe."
Bikin ranar nasara na shekara-shekara na Rasha na nuna ranar da Tarayyar Soviet ta doke Jamus a Yaƙin Duniya na Biyu, da kuma girmama ’yan ƙasar Soviet miliyan 27 da suka mutu a yaƙin.

Source: Getty Images
An yi faretin sojoji a Moscow
A karon farko, faretin na ranar Asabar ya haɗa da dakarun sojoji daga Koriya ta Arewa, a matsayin karramawa ga kasar kan turo sojojinta don yaƙi tare da dakarun Moscow domin fatattakar farmakin da Ukraine ta kai yankin Kursk na Rasha.
Dakarun Rasha sun kwashe fiye da shekaru huɗu suna yaƙi a Ukraine. Wannan lokaci ya fi tsawon lokacin da dakarun Soviet suka yi suna yaƙi a Yaƙin Duniya na Biyu, wanda a Rasha aka sani da Babban Yaƙin Kishin Ƙasa na 1941-45.
Putin ya gana da Donald Trump
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya yi wata ganawa da takwaransa na Amurka, Donald Trump.
Donald Trump ya bayyana cewaya bayyana cewa ya yi wata doguwar tattaunawa da shugaban Rasha, Vladimir Putin.
Daga cikin batutuwan da suka mayar da hankali a kai har da yiwuwar ɗan gajeren tsagaita wuta a yaƙin Ukraine da ake gwabzawa.
Asali: Legit.ng

