Ana Fargabar Sabon Harin Sojoji Ya Kashe Mutanen Gari a Jihar Neja
- Jama'a sun shiga fargaba bayan zargin wani harin sojojin saman Najeriya sun bi 'yan ta'adda zuwa kauyen Guradnayi da ke jihar Neja
- Ana tsoron an hallaka fararen hula 'yan ba ruwana da dama a wani sabon harin sama da aka kai a ƙauyen a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayu, 2026
- Mazauna yankin sun ce harin ya faru ne yayin da jirgin soji ke bin ‘yan ta’adda da suka ratsa yankin, kuma sun ci gaba da ta'addancinsu duk da harin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger – Rahotanni daga jihar Neja sun nuna cewa an sake kashe fararen hula da dama a wani harin sama da aka kai ƙauyen Guradnayi da ke kusa da Kusasu a ƙaramar hukumar Shiroro.
Mazauna yankin sun shaida cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi 10 ga watan Mayu, 2026 yayin da jiragen yaƙin sojoji ke bin wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne da suka ratsa yankin a kan babura.

Source: Getty Images
Jaridar Premium Times ta kawo labarin cewa wani mazaunin Kusasu mai suna Auta Awododo ya ce harin ya auku ne da misalin 5.00 na safe.
Sojoji sun kai hari jihar Neja
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa ana zargin mutane akalla 12 sun mutu a gidan 'yan wansu da ke Guradnayi bayan an kai harin.
Majiyoyi daga yankin sun ce jirgin sojin ya fara jefa bam kusa da kogin Kusasu kafin daga bisani aka sake jefa wani bam a Guradnayi.
A cewar Auta Awododo, duk da cewa ana zargin an kashe wasu ‘yan ta’adda a harin na baya-bayan nan, fararen hula ne suka fi shan wahala.
Wata majiya daga ƙungiyar masu sintiri ta yankin ta ce ‘yan ta’addan sun tsallaka daga Shiroro zuwa ƙaramar hukumar Munya bayan harin.
Majiyar ta ƙara da cewa:
“Yanzu haka suna aiki a Kabula kusa da Kuchi. Har yanzu ba a tabbatar da sace mutane ko kashe-kashe ba, amma sun sace shanu masu yawa daga al’ummomi daban-daban a Munya.”
Wani mazaunin yankin ya ce:
“Sojoji sun fara jefa bam kusa da kogin Kusasu. Bam na biyu kuma aka jefa shi a Guradnayi.”
Jama'ar yankin sun bayyana cewa sun shiga cikin tashin hankali marar misaltuwa, duk da cewa yan ta'adda aka biyo suka bi ta yankinsu.
Ana dakon martanin sojoji
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojin saman Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba. Haka kuma kakakin rundunar, Ehimen Ejodame, bai amsa tamabayoyin manema labarai ta sakonni da aka aika masa ba.
Sai dai wani ɗan siyasa daga yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya nuna takaici kan yadda ake ci gaba da rasa rayukan fararen hula sakamakon hare-haren sama.
Ya ce:
“Abin da ya fi ciwo shi ne, wannan ba shi ne karo na farko da irin wannan abu ke faruwa ba.”
A shekarar 2022 ma, wani jirgin yaƙin rundunar sojin saman Najeriya ya kashe yara shida a ƙauyen Kurebe da ke Shiroro. Bayan watanni biyar kuma, wani sabon harin sama ya kashe fararen hula takwas a ƙauyen guda.
Sojoji sun yi ram da babban 'dan ta'adda
A baya, mun kawo labarin cewa dakarun Operation Fansan Yamma sun kama wani da ake zargin dan bindiga ne a Birnin Gwari tare da kwato manyan makamai a yayin aikin.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa daga cikin abubuwan da aka samu a wurinsa akwai bindigar AK-47, wayoyi da tabar wiwi yayin da aka samu nasara a kan 'yan ta'addan da aka gwabza da su.
Binciken farko da jami’an tsaro suka yi ya gano hotunan da ake zargin mutumin yana sanye da kayan soji tare da daukar hoto da bindigar PKT, kuma ya shiga hannu domin ci gaba da fuskantar bincike.
Asali: Legit.ng


