Tsohon Minista daga Arewa Ya Rasu, Gwamnonin yankin Sun Tuna Alherinsa
- Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya ta yi alhinin rasuwar tsohon Ministan Kudi a kasar, Alhaji Abubakar Alhaji
- Gwamna Inuwa Yahaya ya ce marigayin ya taka muhimmiyar rawa a Ma'aikatar Tsare-tsaren Kasa, Ma'aikatar Kudi da kuma sauran mukamai
- Gwamnonin Arewa sun miƙa ta'aziyya ga iyalansa, Sarkin Musulmi, gwamnatin Sokoto da daukacin 'yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya (NNGF) ta yi martani game da rashin da aka yi na tsohon minista a Najeriya.
Kungiyar ta bayyana alhini kan rasuwar tsohon Ministan Kudi kuma Sardaunan Sokoto, Alhaji Abubakar Alhaji, wanda ya rasu ranar Alhamis a Abuja.

Source: Facebook
Hakan na cikin sakon ta'aziyya da sakataren shugaban kungiyar, Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana a Facebook.
Sardaunar Sokoto: Gwamnonin Arewa sun yi jimami
Sanarwar ta tabbatar da marigayin a matsayin fitaccen jami'in gwamnati kuma dattijo mai kishin kasa wanda ya ba da gudunmawa sosai.
Ya tuna cewa Alhaji Abubakar Alhaji ya yi aiki a matsayin Ministan Tsare-tsaren Kasa kafin daga baya ya zama Ministan Kudi a gwamnatin Janar Ibrahim Babangida.
Gwamnan ya ce marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin tattalin arzikin Najeriya, inda ya ba da gudummawa mai yawa ga ci gaban kasa.
Ya kuma bayyana cewa bayan kammala aikinsa na minista, an naɗa shi Babban Kwamishinan Najeriya a Birtaniya a shekarar 1992, inda ya ci gaba da yi wa kasa hidima.
Inuwa Yahaya ya kuma yaba wa marigayin saboda asalinsa na zuri'ar Shehu Usmanu Danfodiyo, yana mai cewa ya kasance mai kare tarihi da al'adun Daular Usmaniyya ta Sakkwato.
Sanarwar ta ce:
"A madadin gwamnonin jihohin Arewa 19, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na III, da daukacin Masarautar Sokoto, da gwamnati da al’ummar Sokoto, tare da dukkan ’yan Najeriya da ke jimamin rasuwar wannan fitaccen dattijin ƙasa."

Source: Facebook
Ta'aziyyar gwamnonin Arewa ga iyalan tsohon minista
Gwamnan ya ce rasuwar Alhaji Abubakar Alhaji babban rashi ne ga iyalansa, al'ummar Sokoto, Arewacin Najeriya da kuma kasa baki ɗaya saboda kwarewarsa da nagartaccen shugabanci.
A madadin gwamnonin jihohin Arewa 19, Gwamna Inuwa Yahaya ya miƙa ta'aziyya ga iyalan marigayin, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar na Uku da Daular Usmaniyya.
Haka kuma ya jajanta wa gwamnatin da al'ummar Sokoto tare da dukkan 'yan Najeriya da ke alhinin rasuwar wannan fitaccen dattijo mai hidimar kasa.
Sakon ya ƙare da addu'ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa Alhaji Abubakar Alhaji kura-kuransa, Ya saka masa da Aljannar Firdausi bisa rayuwar hidimar da ya yi wa Najeriya.
Tsohon babban alkali ya rasu a Borno
Mun ba ku labarin cewa an shiga jimami bayan sanar da rasuwar tsohon alkalin Babbar Kotun Tarayya daga jihar Borno da ke Arewacin Najeriya.
Mai shari'a Babagana Ashigar, ya rasu a Maiduguri bayan gajeruwar rashin lafiya, lamarin da ya jawo alhini tsakanin ma'aikatan shari'a da iyalansa.
An yi jana'izarsa ranar Asabar bisa koyarwar addinin Musulunci, yayin da Babbar Kotun Tarayya ta bayyana cewa ya yi aiki da gaskiya.
Asali: Legit.ng

