JAMB: Kotu Ta Yi Hukunci kan 'Hana' Mata Dalibai Rubuta Jarabawa da Hijabi

JAMB: Kotu Ta Yi Hukunci kan 'Hana' Mata Dalibai Rubuta Jarabawa da Hijabi

  • Babbar Kotun Oyo ta yanke game da zargin tilasta dalibai mata Musulmi cire hijabi kafin rubuta jarabawar UTME
  • Kotun ta ce tilasta cire hijabi ya take 'yancin addini, sannan ta umarci JAMB da PEFTI su ba mai karar hakuri tare da biyan diyya ta Naira miliyan 10
  • Hukuncin ya biyo bayan karar wata daliba da aka hana rubuta jarabawar UTME ta 2025 har sai ta cire hijabi, lamarin da ya jawo maganganu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Babbar Kotun Jihar Oyo ta yi zama game da shari'ar da ae yi na hana dalibai saka hijabi a jarabawar UTME.

Kotun ta yanke hukuncin cewa Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu, JAMB, ba ta da ikon tilasta wa dalibai mata Musulmi cire hijabinsu kafin rubuta jarabawar.

Kara karanta wannan

APM ta ce Tinubu ya tara malaman addini ya sharara masu karya

Kotu ta yi hukunci an hana mata saka hijabi a jarabawar UTME
Daliba mai hijabi da ake ce an hana shiga rubuta JAMB. Hoto: Northern Magazine.
Source: Facebook

Kotun ta bayyana cewa wannan mataki ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya, saboda yana tauye 'yancin kowa na bin addininsa cikin walwala ba tare da takura ba, cewar Vanguard.

JAMB: Hukuncin da kotu ta yanke

Mai shari'a Y. S. Adekunle ya yanke hukuncin ne a ranar 20 ga Yuli, 2026, bayan Lawal Hameedat Adenike Olamide ta shigar da kara ta hannun mahaifiyarta.

Mai karar ta ce an hana ta rubuta jarabawar UTME da aka gudanar ranar 25 ga Afrilu, 2025, sai dai idan ta cire hijabin da take sanyawa saboda addininta.

Kotun ta kuma samu cibiyar jarabawar PEFTI Film Institute Ltd da laifi tare da JAMB, saboda take hakkin mai karar na samun 'yancin gudanar da addininta.

Mai shari'a ya bayyana cewa duk wata doka ko ka'ida da ke tilasta cire hijabi ga dalibai mata Musulmi kafin rubuta jarabawar JAMB ba ta da inganci kuma ta saba wa kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

'Babu yan bindiga a Niger': Gwamnati ta gano yadda aka samu rashin tsaro

Kotun ta ce matakin da aka dauka ya karya tanade-tanaden Sashe na 38 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wanda ke kare 'yancin addini da gudanar da ibada.

Kotu ta fayyace ikon JAMB kan tilasta cire hijabin mata dalibai
Dalibaida ke rubuta jarabawar UTME a Najeriya. Hoto: @JAMBHQ.
Source: Facebook

Umarnin da kotu ta ba hukumar JAMB

A hukuncin, kotun ta umarci hukumar JAMB da PEFTI su rubuta takardar neman afuwa daban-daban ga mai karar, sannan su wallafa afuwar a jaridu biyu na kasa cikin kwanaki bakwai.

Bugu da kari, kotun ta ba da umarnin a biya mai karar diyyar Naira miliyan 10 tare da karin Naira dubu 500 a matsayin kudin shari'a, cewar Daily Post.

Mai shari'a Adekunle ya bayyana cewa an jinkirta yanke hukuncin domin duba sabon hukuncin Kotun Daukaka Kara kan irin wannan batu kafin a cimma matsaya ta karshe.

JAMB: Ana zargin an hana Musulmai saka hijabi

Mun ba ku labarin cewa malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana kan zargin hana wata daliba shiga dakin rubuta JAMB.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a wata cibiyar da ake rubuta jarrabawar a Oyo, ina ana hana dalibar shiga ciki saboda sanya hijabi.

Kakakin hukumar JAMB na kasa, Fabian Benjamin ya yi karin haske kan abubuwan da suka faru da matakin da aka dauka a hukumance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.