Remi Tinubu Ta Lallaba Saudiyya, Tana So a Taimaka wa Najeriya kan Karatun Allo

Remi Tinubu Ta Lallaba Saudiyya, Tana So a Taimaka wa Najeriya kan Karatun Allo

  • Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, ta roƙi Saudiyya ta taimaka wajen inganta ilimin Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya
  • Ta ce rashin ilimantar da Almajirai da sauran yara masu zaman gida na iya ƙara matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasar
  • Jakadan Saudiyya a Najeriya ya bayyana cewa ƙasashen biyu suna da dangantaka mai ƙarfi, tare da nuna shirinsu na ƙara faɗaɗa haɗin gwiwar tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja - Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta buƙaci Masarautar Saudiyya ta haɗa hannu da Najeriya wajen gyara tsarin ilimin allo da kuma yaran da ba sa zuwa makaranta.

Ta ce rashin bai wa waɗannan rukunin yara ilimi na zamani na iya zama babbar barazana ga tsaron ƙasa.

Oluremi Tinubu ta nemi Saudiyya ta taimakawa Najeriya kan karatun Allo
Oluremi Tinubu tare da jakadan Saudiyya a Najeriya a Yousef Mohammed, a fadar shugaban kasa Abuja. Hoto: @KSAembassyNG
Source: Twitter

Remi Tinubu ya so a gyara karatun allo

Kara karanta wannan

Saudiyya ta shiga tsaka mai wuya, Iran ta matsa mata lamba ta fannoni 3 a yaki da Amurka

Uwargidan shugaban ƙasar ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ta karɓi jakadan Masarautar Saudiyya a Najeriya, Yousef Mohammed Al-Balawi, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, in ji rahoton Punch.

A cikin wata sanarwa da babbar mataimakiya ta musamman kan harkokin yaɗa labarai ga uwargidan shugaban ƙasa, Busola Kukoyi, ta fitar, an bayyana cewa Oluremi Tinubu ta nemi haɗin gwiwar Saudiyya wajen taimaka wa yaran Almajirai.

Remi ta fadi damuwarta kan Almajiranci

A cewarta, haɗin gwiwar zai mayar da hankali ne kan haɗa koyarwar Larabci da addinin Musulunci da kuma ilimin boko.

Ta ce wannan tsarin ya dace da tsarin Almajiranci, wanda ya ta'allaka ne kan koyar da Alƙur'ani amma bai cika haɗuwa da ilimin zamani ko koyon sana'o'i ba.

Ta ce:

"Ina aiki tare da mata da yara marasa galihu a cikin al'umma. Ina matuƙar tausaya wa yaran Almajirai da ke Arewacin Najeriya. Ina ganin suna buƙatar kulawa ta musamman.
"Yawancin matsalolin tsaro da ake fama da su a ƙasar nan, idan ba a kula da irin waɗannan yara ba, ban san abin da zai faru nan gaba ba.

Kara karanta wannan

Yaki da yunwa: Oluremi ta fadi yadda Tinubu ya tallafa wa yan kasa da abinci

"Ina ganin har yanzu akwai damar fara ba su ilimin boko. Idan muka samu damar yin hakan, makomar Najeriya za ta kasance cikin aminci."

An yabi dangantakar Najeriya da Saudiyya

Uwargidan shugaban ƙasar ta bayyana cewa tana da kwarin gwiwar Saudiyya za ta kasance abokiyar hulɗa mai kyau wajen aiwatar da wannan shiri, tana mai nuni da daɗaɗɗiyar dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu ta fuskar addini da al'adu.

Ta ce haɗin gwiwar zai taimaka wajen haɗa koyarwar addinin Musulunci da ilimin boko ba tare da tauye martaba da asalin tsarin Almajiranci ba.

Uwargidan shugaban kasa ta ce idan ba a gyara tsarin karatun allo ba za a iya samun karuwar matsalar tsao.
Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Oluremi Tinubu tana jawabi a wani taro. Hoto: @SenRemiTinubu
Source: Facebook

Jakadan Saudiyya ya yi magana

A nasa jawabin, jakadan Saudiyya, Yousef Mohammed Al-Balawi, ya ce ya shafe watanni biyar a Najeriya kuma ya gamsu da irin tarbar da ya samu daga jami'an gwamnati.

Ya bayyana cewa Najeriya da Saudiyya suna da alaƙa mai ƙarfi ta fuskar tarihi, addini da al'adu, yana mai cewa akwai damar ƙara bunƙasa dangantakar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu.

Jakadan ya ƙara da cewa ganawar da ya yi da mambobin Majalisar Zartarwa ta Tarayya tun bayan zuwansa Najeriya za ta taimaka wajen ƙara ƙarfafa ci gaban ƙasashen biyu.

Kara karanta wannan

An daura auren gata ga mutum 300 a Kebbi, gwamnati za ta cigaba da shirin

Duba hotunan ziyarar da aka wallafa a shafin jakadancin Saudiyya a Najeriya na X a kasa:

"Ba a koyon karatu da bara" - Sarkin Musulmai

A wani labari, mun ruwaito cewa, mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya yi kira na musamman kan kawo gyara a harkar almajiranci.

Alhaji Sa'ad Abubakar III ya yi magana ne a yayin wani taron kaddamar da makarantar karatun Alkur'ani ta zamani.

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi karin haske kan yadda aka gina makarantar da yadda za a kara wasu nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com