MURIC Ta Goyi Bayan Pantami, Ta Soki Tsarin APC a Zaben Dan Takarar Gombe
- Kungiyar MURIC da Forum for Justice of Nigeria sun goyi bayan Farfesa Isa Ali Pantami kan matsayarsa a zaben fitar da gwani
- MURIC ta ce tana tare da yin watsi da tsarin sulhun APC na zaben gwamnan Gombe na zaben shekarar 2027
- Kungiyar ta ce tsarin sulhun da aka gudanar ba tare da sanin Pantami ba ya saba da dimokuradiyya, dokar zabe da kuma adalci tsakanin masu neman takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC da Forum for Justice of Nigeria sun yi magana kan zaben fitar da gwani a Gombe.
Kungiyoyin sun bayyana goyon bayansu ga tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, tare da sukar tsarin sulhun APC na zaben gwamnan Gombe na shekarar 2027.

Source: Twitter
MURIC ta goyi bayan Farfesa Pantami
Kungiyoyin sun bayyana hakan ne a cikin sanarwa daban-daban da suka fitar a Abuja, inda suka ce tsarin sulhun da ake zargin an gudanar ya saba da ka’idojin dimokuradiyya, cewar Tribune.
MURIC ta yi watsi da tsarin sulhun, tana mai cewa an gudanar da shi ba tare da halartar Pantami ko saninsa ba duk da kasancewarsa daya daga cikin manyan masu neman takarar gwamna.
A cikin sanarwar da shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce duk wani tsarin sulhu da bai hada da dukkan masu neman takara ba ya saba da kundin tsarin dimokuradiyya da dokar zabe.
“Rahotanni sun nuna cewa APC ta Gombe ta gudanar da tsarin sulhu mai son rai ba tare da halartar ko sanin daya daga cikin manyan masu neman takara ba, wato Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami,”
- In ji sanarwar.

Kara karanta wannan
Pantami ya bayyana muhimmancin zaben fitar da gwani ga jam'iyyar APC, ya yi gargadi
Kungiyar ta ce hakan rashin adalci ne kuma ya saba da tsarin dimokuradiyya, tana mai bukatar a samar da dama iri daya ga duk masu neman takara.

Source: Twitter
Yadda MURIC a yi zaben fitar da gwani
MURIC ta kara da cewa duk wani tsarin sulhu zai kasance sahihi ne kawai idan duk wadanda aka tantance sun amince a rubuce su janye daga takara, in ba haka ba sai a gudanar da zaben fidda gwani kai tsaye.
Kungiyar ta kuma nuna damuwa cewa gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da wanda ake zargin an tsayar ta hanyar sulhu duk daga mazaba daya suka fito.
Ta bambanta Pantami da wanda aka fi so a tsarin sulhun, tana cewa tsohon ministan ya kasance mai biyayya ga APC tsawon lokaci sabanin wasu ‘yan siyasar da suka dade suna sauya jam’iyya.
MURIC ta ce Pantami yana da gagarumar karbuwa a tsakanin al’umma musamman ta hanyar tafiyar “Pantamiya”, wanda ta ce zai taimaka wa APC samun nasara a zabe, cewar Daily Post.
Hakazalika, Forum for Justice of Nigeria ta yaba wa Pantami kan matsayinsa na goyon bayan adalci, dimokuradiyya a cikin jam’iyya da kuma siyasa cikin lumana.
A sanarwar da shugabanta, Farfesa Ahmad Adamu ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce kalaman Pantami sun nuna muhimmancin adalci da dimokuradiyya ga zaman lafiyar siyasar Najeriya.
Kungiya ta koka da kalaman Pantami
Kun ji cewa wata kungiya a Najeriya ta soki kalaman da aka danganta da Farfesa Isa Ali Pantami kan zaben fitar da gwani na APC a Gombe.
Ƙungiyar ta yi gargadin cewa irin wadannan furuci na iya haddasa tashin hankali da barazana ga dimokuradiyya.
Ta ce dole ne a gudanar da zabubbuka cikin gaskiya da lumana, ba tare da amfani da barazana, tsoratarwa ko tayar da rikicin siyasa ba.
Asali: Legit.ng

