Yan Sandan Kano Sun Damke Dilan Makamai, An Kwato Manyan Bindigu

Yan Sandan Kano Sun Damke Dilan Makamai, An Kwato Manyan Bindigu

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani da ake zargi da safarar makamai a ƙaramar hukumar Dala tare da gano wasu miyagun makamai
  • Mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa an ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda uku da harsasai tare da karin wasu makaman
  • ‘Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya amsa cewa ya samo makaman ne daga jihar Katsina yayin da ya ke ci gaba da ba su bayanai a kan safarar makaman da ya ke yi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da kama wani mutum da ake zargi da safarar makamai tare da ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda uku da aka ƙera a gida a ƙaramar hukumar Dala.

Kara karanta wannan

APC ta tara N4.4bn daga sayar da fam na takarar 2027 duk da rikicin jam'iyya

Jami’an rundunar sun ce an gudanar da samamen ne ta hannun dakarun sashen yaƙi da masu garkuwa da mutane a unguwar Dandinshe a ranar Juma’a 8 ga watan Mayu, 2026.

Yan sanda sun kama mai safarar makamai a Kano
Kwamishinan yan sandan Kano, Ibrahim Bakori Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi 10 ga watan Maris, 2026 kuma ya wallafa a shafinsa na Facebook

Ya sanda sun kama matashi a Kano

A cewar sanarwar, jami’an tsaro sun kama wanda ake zargi, mai suna Umar Danladi Usman mai shekaru 35, mazaunin Kurna Layin Masallacin Juma’a, yayin da yake tuka mota ƙirar Honda Accord mai gilashi baki.

Rundunar ta ce bayan binciken da aka gudanar a jikinsa da kuma cikin motar, jami’an suka gano bindigu ƙirar AK-47 guda uku da aka ƙera a gida.

Haka kuma an gano harsasai biyar, kwanson harsashi guda ɗaya, wuƙaƙe guda uku, takalman sojoji da kuma katin shaidar ɗan sanda da ake zargin na bogi ne.

Sanarwar ta ce:

“Samamen ya kai ga cafke Umar Danladi Usman mai shekaru 35 daga yankin Kurna Layin Masallacin Juma’a.”

Kara karanta wannan

Yaron Atiku Abubakar ya sayi fam a ADC, zai nemi takarar sanata a Adamawa

Yan sandan Kano sun zurfafa bincike

Rundunar ‘yan sandan ta kuma bayyana cewa yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya samo bindigun ne daga ƙaramar hukumar Dutsin-Ma da ke jihar Katsina.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

“Ya amsa cewa ya samo bindigun da aka ƙera a gida daga ƙaramar hukumar Dutsin-Ma ta jihar Katsina. A halin yanzu yana tsare a hannun ‘yan sanda yayin da ake ci gaba da bincike domin kamo sauran waɗanda ake zargi da hannu tare da tarwatsa hanyar safarar makaman.”

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa abin da ya kira ƙwarewa da jarumtaka.

CP Bakori ya ce nasarar kamen na nuna yadda sauye-sauyen da ake yi a rundunar ‘yan sanda ke taimakawa wajen yaƙi da manyan laifuffuka ta hanyar amfani da bayanan sirri da inganta dabarun aiki.

'Yan bindiga sun hallaka mutum a Kano

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun ci karo da sojoji da yan sanda a jihar Kano

A baya, mun kawo labarin cewa 'yan bindiga sun shiga yankin karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano, sun kashe mutum daya tare da sace shanu sama da 300 tare da jefa jama'a a cikin tsoro.

Kansilan mazabar Mainika, Auwal Abdussalam Barau ya ce sojoji da yan bijilanti sun kwato kusan shanu 100 daga hannun maharan duk d barnar da suka fara aikata wa a kauyen da ke Gwarzo.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce dakarunta da yan JTF sun fatattaki 'yan bindigan tare da bawa jama'a tabbacin cewa ana aiki tukuru domin tsare rayukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng