Shugaban Sojin Iran Ya Gana da Mojtaba Khamenei, an Ji Abin da Suka Tattauna
- Sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya gana da shugaban rundunar sojin kasar tare da bayar da sababbin umarni
- Rahotanni sun ce rundunar Iran ta bayyana cikakken shirin tunkarar duk wani hari daga Amurka da Isra’ila cikin gaggawa
- Rashin bayyanar Mojtaba Khamenei a bainar jama’a tun bayan nada shi ya kara jawo ce-ce-ku-ce da tambayoyi kan halin da yake ciki a Iran
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Sabon jagoran addini a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei ya gana da shugaban rundunar hadin gwiwar sojojin kasar.
An yi ganawar ce domin tattauna sababbin matakan ci gaba da ayyukan soja kan makiya, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Source: Getty Images
Shugaban soji ya gana da Mojtaba Khamenei
Rahoton Times of Israel ya ce shugaban rundunar Ali Abdollahi ya yi wa Khamenei bayani kan yadda dakarun kasar suka shirya a yakin da ake yi.

Kara karanta wannan
Yakin Iran da Isra'ila: An 'gano' kasar da tafi cin moriyar rikicin fiye da Amurka
Ya ce dakarun na kan shiri a kowane lokacin domin fuskantar duk wani hari daga Amurka ko Isra’ila a yankin Gabas ta Tsakiya wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma.
A cewar rahoton, Abdollahi ya bayyana cewa sojojin Iran suna cikin shirin ko-ta-kwana, yana mai gargadin cewa duk wata kuskure daga makiya zai fuskanci mayar da martani cikin gaggawa.
Ya ce:
“Sojojinmu suna shirye domin fuskantar duk wani mataki daga makiya irin Amurka da yahudawan Isra’ila.
Idan makiya suka yi wani kuskure, martanin Iran zai kasance cikin gaggawa, tsanani da kuma mataki mai zafi.”

Source: Facebook
Ana kokwanton halin lafiyar Mojtaba Khamenei
Rahotannin sun nuna cewa har yanzu ba a ga ko jin sabon jagoran Iran a bainar jama’a ba tun bayan nadin da aka yi masa a watan Maris na shekarar 2026, cewar Al Jazeera.
Wannan lamarin ya jawo karin ce-ce-ku-ce a cikin kasar da kuma kasashen waje, inda mutane ke tambayar ko yana cikin koshin lafiya da kuma cikakken iko.
Kafafen yada labarai na Iran sun ce gwamnatin kasar na ci gaba da sanya ido kan duk wani motsi daga Amurka da Isra’ila yayin da rikicin yankin ke kara tsananta.
Rahotanni sun kara da cewa Iran ta jaddada aniyarta ta kare kanta daga duk wani hari, tana mai cewa dakarunta sun shirya tsaf domin kare muradun kasar a kowane lokaci.
Iran ta gargadi Amurka kan jiragen ruwanta
A baya, an ji cewa rundunar IRGC ta Jamhuriyar Musulunci a Iran ta yi barazanar kai munanan hare-hare kan sansanonin Amurka da jiragen ruwanta idan har ta kuskura ta farmake ta.
Iran ta yi wannan gargadi ne ga kasar idan ta kai hari kan tankokin mai ko jiragen kasuwancin kasar wanda ka iya jawo martani mai zafi kan lamarin a yakin da ake yi.
Rikicin Iran da Amurka tare da Isra’ila ya kara tsananta bayan hare-haren da aka kai tun watan Fabrairu, lamarin da ya haddasa martanin Tehran da rikicin mashigar Hormuz.
Asali: Legit.ng
