Latest
Sojojin Isra’ila biyu sun mutu, yayin da wasu bakwai suka jikkata bayan fashewar bam a wani gini da aka yi wa tarko a kudancin Lebanon a Gabas ta Tsakiya.
Mutane 176 da aka sace a harin Woro da Nuku a jihar Kwara sun samu 'yanci bayan watanni, yayin da gwamnatin jihar ta yabawa Tinubu da jami'an tsaro.
Adam Fakai, fitaccen masoyin Bola Tinubu a Kebbi, ya dakatar da tallata ayyukan gwamnatin tarayya, yana mai zargin rashin kulawa da goyon baya daga APC.
Gwamnatin Osun karkashin jagorancin Adeleke ta sake raba tallafin rage raɗaɗin tsadar rayuwa ga ma’aikatan gwamnati, domin ƙara musu albashi da inganta jin daɗinsu.
Sakataren ADC na ƙaramar hukumar Gombe ya yi murabus tare da komawa PDP domin mara wa Farfesa Isa Ali Pantami baya a takarar gwamnan Gombe ta 2027.
Farfesa Rabia Sa’id ta jami'ar BUK da ke Kano ta ce nadin da aka yi mata a kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan illolin yaƙin nukiliya ba sabon abu ba ne.
Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya kalubalanci shugaban EFCC kan daskare asusun jihar, yana zargin hukumar da ɗaukar matakin ba tare da umarnin kotu ba.
'Yan bindiga sun kashe 'yan sintiri uku 'yan uwa a Riyom, Plateau, yayin sintirin dare, lamarin da ya jawo kira ga hukumomin tsaro su dauki mataki.
Dakarun rundunar sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 14 daga hannun ƴan bindiga tare da ƙwato dabbobi 281 a wani samame da suka kai a jihar Sokoto.
Masu zafi
Samu kari