Yan Kwankwasiyya, Obidents Sun Shirya Tara Miliyoyi saboda Takarar Obi, Kwankwaso
- Masoyan tsofaffin ƴan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun fara shirin neman mafita game da zaben 227
- Ƴan Kwankwasiyya da Obidienta suna shirin haɗa kai domin takarar shugaban ƙasa a 2027, suna ganin haɗin gwiwa zai kayar da jam’iyya mai mulki
- Jagoran Obidient Movement, Yunusa Tanko, ya ce magoya baya za su tara miliyoyi domin sayen fom ɗin takarar haɗaka ta Obi da Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Masoyan Peter Obi da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso na shiri kan zaben 2027.
Yan Kwankwasiyya da Obidients sun amince su yi aiki tare domin samar da haɗakar tikitin shugaban ƙasa kafin zaɓen 2027.

Source: Twitter
Shirin da Kwankwasiyya, Obidients ke yi
Rahoton Arise TV ya ce mutanen sun bayyana cewa haɗin kai ne kaɗai zai taimaka wajen kayar da jam’iyya mai mulki a Najeriya.
An bayyana wannan matsaya ne a taron masu neman takara na NDC da aka gudanar a Abuja inda ƙungiyoyin Obidient da Kwankwasiyya suka ce za su tattara kuɗaɗe domin tallafa wa haɗakar takarar.
Sun ce jama’a da dama na son shugabanci mai nagarta da gaskiya.
Jagoran Obidient Movement Worldwide, Dakta Yunusa Tanko, ya ce magoya baya za su tara Naira miliyan 60 domin sayen fom ɗin takarar haɗin gwiwa ga Obi da Kwankwaso.
Ya ce wannan mataki yana nuna yadda talakawa suka fara yarda cewa haɗin kai zai ƙara musu ƙarfin nasara.
Tanko ya bayyana cewa haɗakar ta samo asali ne daga buƙatar jama’a na samun shugabanci nagari da kuma wata madadin gwamnati ta gaskiya.
Ya ce mutane daga yankuna daban-daban suna nuna sha’awar mara wa wannan haɗaka baya domin kawo sauyi a ƙasar.

Source: Facebook
Shawarar da aka ba masu neman takara
Da yake jawabi a madadin Peter Obi, Cif Peter Ameh, ya bukaci masu neman takara su rungumi gaskiya, sadaukarwa da shugabanci mai kula da talakawa.
Ameh ya yi gargaɗi kan rikici, sayen ƙuri’u da magudin zaɓe, yana cewa shugabanci na gari yana farawa ne daga gaskiya da amana.
Ya ƙara da cewa duniya da kuma ’yan Najeriya na kallon yadda ’yan siyasa za su gudanar da harkokinsu.
Ya kuma soki sauya sheƙar ’yan siyasa bayan cin zaɓe, yana mai cewa hakan na karya amincewar masu zaɓe tare da raunana dimokuraɗiyya.
Shi ma jagoran Kwankwaso National Network, Moshood Shittu, wanda ya wakilci Kwankwaso, ya ce matsalolin Najeriya sun samo asali ne daga rashin shugabanni masu gaskiya da kishin ƙasa.
Peter Obi ya magantu kan bambancinsa da Kwankwaso
A baya, an ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya bayyana bambancinsa da sauran masu neman shugabancin Najeriya.
Dan siyasar ya bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fi shi samun matsayi a fannin ilmi inda yake da PhD.
Hakazalika, Peter Obi, ya bayyana cewa Najeriya tana bukatar shugaba irinsa wanda ya kware wajen samar da arziki.
Asali: Legit.ng

