Ana Zargin Tinubu Ya Sake Samun Matsala da Shettima, Zai Iya Shafar Kujeransa

Ana Zargin Tinubu Ya Sake Samun Matsala da Shettima, Zai Iya Shafar Kujeransa

  • Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa Bola Tinubu na dab da yanke hukunci kan wanda zai zama mataimakinsa a zaɓen 2027
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan makomar Kashim Shettima a zaben shekarar 2027
  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu a fadar shugaban ƙasa sun nuna rashin jin daɗi bayan Shettima ya raka Hope Uzodinma wajen miƙa fom ɗin takarar Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ana hasashen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na shirin bayyana wanda zai kasance mataimakinsa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Rahotanni sun nuna cewa ana kokarin sasanta rikicin siyasa da ya shafi mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima.

Ana zargin matsala ta barke tsakanin Tinubu da Shettima
Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima yayin taron siyasa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Rahoton Punch ya ce hakan na zuwa bayan wasu matsaloli da suka taso tsakanin bangarorin biyu a watannin baya.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke a Kaduna, zaben fitar da gwani ya jefa shugaban APC a matsala

Musabbabin dawowar rikicin Tinubu da Shettima

Majiyoyi sun bayyana cewa rikicin ya sake ɓarkewa ne lokacin da shugaban dandalin gwamnoni na APC, Hope Uzodinma, ya karɓi fom ɗin takarar Tinubu domin kaiwa sakatariyar jam’iyyar APC tare da Shettima.

Wasu jami’a a fadar shugaban ƙasa sun nuna rashin jin daɗi kan yadda aka bai wa Shettima damar fitowa fili a wajen miƙa fom ɗin.

Rahotanni sun ce wasu mutane a fadar shugaban ƙasa sun ɗauki matakin bincikar Uzodinma domin tabbatar da biyayyarsa ga tsarin siyasa na shugaban ƙasa.

An bayyana cewa ba a nemi a cire shi daga shugabancin gwamnoni gaba ɗaya ba, sai dai an so a “girgiza shi kaɗan” saboda rawar da Shettima ya taka.

Wata majiya ta ce bayyanar Shettima a wajen miƙa fom ɗin ta sa mutane suka fara tunanin cewa Tinubu ya riga ya amince da shi a matsayin abokin takara na 2027.

Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin APC, musamman ganin cewa har yanzu ana tattaunawa kan wanda zai dace da kujerar mataimakin shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

An dora Hayatu Deen a gaban Atiku, Obi da Amaechi a takarar zama shugaban kasa a 2027

Ana tunanin Shettima zai iya rasa kujerar mataimakin shugaban kasa
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Twitter

Ana zargin maye gurbin Shettima a zaben 2027

An ce ana duba yiwuwar maye gurbin Shettima da wasu manyan ‘yan siyasa uku, ciki har da Nuhu Ribadu, Janar Christopher Musa mai ritaya, da tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara.

Ana ganin zaɓin Dogara ko Musa zai taimaka wajen rage korafe-korafen tikitin Musulmi da Musulmi, cewar Leadership.

Sai dai wasu majiyoyi sun gargadi cewa cire Kashin Shettima daga tikitin APC na iya haifar da babbar matsala a Arewa maso Gabas, inda yake da tasiri sosai.

Sun ce hasarar siyasa da hakan zai jawo na iya fiye da ribar da jam’iyyar za ta samu.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa rikicin da ya shafi Uzodinma ya taɓo siyasar gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara.

Tinubu ya magantu kan ikirarin kisan dan ta'adda

Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da kashe babban kwamanda a kungiyar ISIS, Abu-Bilal Al-Manuki a yankin Tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

2027: Tsohon shugaban a INEC ya samu tikiti, zai tsaya takarar gwamnan Yobe a ADC

Tinubu ya ce sojojin Najeriya da taimakon dakarun Amurka ne suka kai samame maboyar yan ta'addan kuma suka samu nasara.

Shugaban kasar ya gode wa Shugaba Donald Trump na kasar Amurka bisa goyon bayan da yake ba Najeriya a yaki da ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.