Maidoki: Sanatan APC a Kebbi Ya Fice daga Jam'iyyar ana Dab da Zaben Fitar da Gwani

Maidoki: Sanatan APC a Kebbi Ya Fice daga Jam'iyyar ana Dab da Zaben Fitar da Gwani

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta rasa daya daga cikin sanatocin da take da su a Majalisar dattawa wadanda suka fito daga jihar Kebbi
  • Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu a Majalisar dattawa, Garba Maidoki, ya sanar da murabus dinsa daga jam'iyyar APC ba tare da bata lokaci ba
  • Murabus din na sa daga APC na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaben fitar da gwani na masu neman takarar sanata a karkashin inuwar jam'iyyar mai mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Kebbi, jihar Kebbi - Sanata Garba Musa Maidoki, mai wakiltar mazaɓar Kebbi ta Kudu a majalisar dattawa, ya yi murabus daga jam’iyyar APC.

Sanata Garba Maidoki ya fice daga APC gabannin zaɓen fitar da gwani na takarar sanata na jam’iyyar da aka tsara gudanarwa ranar Litinin, 18 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Jerin masu neman takarar majalisar tarayya da APC ta yi watsi da su a wurin tantancewa

Sanata Garba Maidoki ya fice daga jam'iyyar APC
Sanata Garba Maidoki a zauren majalisar dattawa Hoto: Senator Garba Maidoki
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Sanata Garba Maidoki ya sanar da murabus ɗinsa ne a cikin wata wasiƙa mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Mayu, 2026.

Sanata Garba Maidoki ya bar APC

An aika da wasikar ga shugaban jam'iyyar APC na mazaɓar Rafin Zuru da ke karamar hukumar Zuru a jihar Kebbi, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.

Sanatan ya ɗora alhakin shawararsa a kan dambarwar cikin gida da ta daɗe tana faruwa a cikin jam’iyyar, inda ya bayyana cewa lamarin ya yi tasiri mara kyau ga burinsa na siyasa.

“Na rubuto ne domin sanar da kai a hukumance game da janyewa ta daga jam’iyyar APC, mazaɓar Rafin Zuru."
“Wannan shawara ta biyo bayan rikice-rikicen cikin gida a cikin jam’iyyar, waɗanda suka ci gaba da haifar da fargaba mai tsanani ga muradina na siyasa."

- Sanata Garba Maidoki

Ya yi wa jam'iyyar APC godiya

Sanata Garba Maidoki ya kuma nuna godiyarsa ga jam’iyyar saboda damar da ta ba shi na yin hidima a ƙarƙashin inuwarta.

Kara karanta wannan

Mahmud Buba: Abin Al'ajabin Zazzau ya janye daga neman takarar dan majalisar wakilai

A halin yanzu, ɗan majalisar yana matsayin shugaban kwamitin Majalisar dattawa kan bin dokokin majalisa kuma mataimakin shugaban kwamitin Majalisar dattawa kan yaɗa labarai da wayar da kan kasa.

Sanata Garba Maidoki ya raba gari da APC
Sanata Garba Maidoki mai wakiltar Kebbi ta Kudu a Majalisar dattawa Hoto: Senator Garba Maidoki
Source: Facebook

Murabus ɗinsa na zuwa ne a tsakiyar dambarwar siyasa da hamayyar cikin gida a cikin APC a jihar Kebbi yayin da jam’iyyar ke shirin zaɓubbukan fitar da gwani na takarar sanata, lamarin da ke rura wutar jita-jita game da yiwuwar sake fasalin ƙawancen siyasa gabannin babban zaɓen 2027.

Yusuf Buhari ya samu tikitin APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, ya samu tikitin takara a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Yusuf Buhari ya lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC a mazabar Daura/Sandamu/Mai'Adua da ke jihar Katsina a tarayyar Najeriya.

Dan tsohon shugaban kasar ya doke abokin hamayyarsa da tazara mai nisa, inda ya samu jimillar ƙuri’u 17,342, yayin da Auwal Lawal Musa ya samu ƙuri’u 480 a faɗin ƙananan hukumomin guda uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng