Kungiyar Kiristoci Ta Fito Gaba Gadi Tana Fada da Tikitin Muslim Muslim a 2027
- Kungiyar Fastoci ta Najeriya (PFN) ta bayyana cewa ba ta goyon bayan tsarin tikitin takarar shugaban kasa na Musulmi da Musulmi a zabukan shekarar 2027
- PFN ta bayyana cewa Najeriya kasa ce mai mabambanta addinai da kabilu, saboda haka ya kamata shugabancin kasar ya nuna wannan adalci da daidaito
- Matakin na zuwa ne biyo bayan matakin jam'iyyar APC na sake tsayar da Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Kungiyar fastoci ta Najeriya ta PFN ta bayyana cewa ba za ta goyi bayan sake tsayar da tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2027 ba.
PFN ta fadi hakan ne ta hanyar wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Dr Sylvanus Ukafia, ya fitar bayan taron majalisar gudanarwa ta kasa (NEC).

Kara karanta wannan
Baraka a APC, tsohon minista ya fadi matsayarsa kan amincewa da zaben fitar da gwani

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto kungiyar ta bayyana cewa wannan tsari ba ya nuna daidaito tsakanin addinai wajen shugabancin kasar, wanda ke da muhimmanci ga hadin kan al'umma.
Matsayar PFN kan tikitin takara
A cikin sanarwar, majalisar gudanarwa ta PFN ta bayyana cewa sun duba halin da kasar ke ciki inda suka yanke shawarar samar da matsaya domin ciyar da kasar gaba.
Sanarwar ta ce:
"PFN ba ta goyon bayan daukar tikitin Musulmi da Musulmi domin rike mukaman zabe. Najeriya kasa ce mai mabambanta addinai da kabilu wadanda ya kamata su samu wakilci a shugabanci.
"Shugabanci mai nuna kula da kowa da kowa yana haɓaka hadin kan kasa, yarda da juna da kuma jin cewa kowa yana da iko."
Tun da Bola Tinubu ya tsaya takara tare da Sanata Kashim Shettima a 2023 ake korafi a fadin Najeriya kan cewa ya kawo tsarin da zai nuna wariyar addini.

Source: Facebook
Batun dokar hana wa'azi
Bayan batun zabe, PFN ta kuma nuna gaba daya adawarta da duk wata doka ko tsari da aka yi niyyar hanawa ko yakure 'yancin wa'azin addinin Musulunci ko Kiristanci a kasar.
Kungiyar ta ce irin wannan doka ta maida hannun agogo baya kuma ta sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya ba kowane dan kasa 'yancin zabar addini, tunani da magana.
Ta roki dukkan bangarorin gwamnati da su kiyaye kundin tsarin mulki tare da kare 'yancin kowa ba tare da nuna bambancin addini ba.
Bayanan fastocin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta fara maganar hana wa'azi a cikin motocin haya domin kaucewa daukar hankalin direbobi.
Kwankwaso ya soki Muslim Muslim
A wani labarin, mun kawo muku cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna damuwa kan yadda Bola Tinubu ya maida hankali wajen rike tikitin Musulmi da Musulmi.

Kara karanta wannan
'Yar Najeriya mai hijabi da nikabi da wasu dalibai sun je China sun ci gasar duniya
Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa wannan batu zai ci gaba da zama babban kalubale a zaben mai zuwa na shekarar 2027.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya bukaci shugaban kasar da ya yi amfani da damar da yake da ita kafin rufe sauya sunayen 'yan takara domin samar da tsari mai daidaito tsakanin al'ummomi.
Asali: Legit.ng
