Tsohon IGP Ya Fallasa Gwamnati, Ya Fadi abin da Ya Jawo Lalacewar Tsaron Najeriya

Tsohon IGP Ya Fallasa Gwamnati, Ya Fadi abin da Ya Jawo Lalacewar Tsaron Najeriya

  • Tsohon sufeta janar na 'yan sanda ya ce gwamnatin tarayya ta raunana ‘yan sanda da gangan ta hanyar kin samar musu da isassun kayan aiki
  • Mike Okiro ya ce rashin ɗaukar sababbin jami’ai na tsawon shekaru biyar ya rage ƙarfin rundunar bayan dubban jami’ai sun bar aiki
  • Tsohon IGP ya buƙaci hukumomin tsaro su riƙa musayar bayanan sirri kai tsaye domin dakile hare-haren masu aikata laifuka cikin gaggawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja - Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mike Okiro (mai ritaya), ya zargi gwamnatin tarayya da gangan da raunana rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta hanyar rashin samar mata da isassun makamai da kayan aiki, yana cewa hakan ya ƙara ta’azzarar matsalar tsaro a ƙasar.

Okiro ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin taron tattaunawa kan tsaro da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan

Yaki da yunwa: Oluremi ta fadi yadda Tinubu ya tallafa wa yan kasa da abinci

Tsohon IGP, Mike Okiro ya ce akwai laifin gwamnati a ta'azzarar matsalar tsaron Najeriya.
Mike Okiro, tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya da ya yi magana kan matsalar tsaro. Hoto: Igbo History
Source: Facebook

An zargi gwamnati kan rashin tsaro

A yayin taron, Okiro ya ce rundunar ‘yan sanda ita ce babbar hukuma da ke kula da tsaron cikin gida, amma gwamnati ta gaza ba ta goyon bayan da ya dace, in ji rahoton Punch.

Ya ce:

“Gwamnati tana ba da gudummawa wajen matsalar tsaro. Rundunar ‘yan sanda ita ce ke jagorantar tsaron cikin gida, amma gwamnati ta raunana ta da gangan. Sakamakon haka shi ne matsalar rashin tsaro.”

Tsohon shugaban rundunar ya ce yanayin tsaro ya sauya, don haka ba zai yiwu jami’in ‘yan sanda ya ci gaba da aiki da tsoffin kayan aiki ba.

“Mun wuce lokacin da ɗan sanda zai riƙa sintiri da sanda kawai. Gwamnati ta samar wa hukumomin tsaro makamai, motocin sulke, na’urorin sadarwa da sauran kayan aikin zamani domin su iya gudanar da aikinsu yadda ya kamata,” in ji shi.

Tsohon IGP ya yi korafi kan daukar jami’ai

Kara karanta wannan

An fitar da hotunan yaran da ake ba horo kan jirage marasa matuka

Okiro ya kuma danganta ƙarancin jami’an ‘yan sanda da rashin ɗaukar sababbin ma’aikata tsawon shekaru.

Ya tuna cewa lokacin da yake shugaban hukumar da ke kula da 'yan sanda (PSC) a shekarar 2013, sun gano cewa ba a ɗauki sababbin 'yan sanda ba na tsawon shekaru biyar duk da cewa jami’ai da dama sun yi ritaya, sun rasu ko suka bar aiki.

Ya ce:

“A lokacin mun gano cewa rundunar ta rasa jami’ai 59,730 ba tare da maye gurbinsu ba. A lokaci guda kuma akwai dubban matasa masu ilimi da ba su da aikin yi."
Mike Okiro ya nemi gwamnatin tarayya ta inganta walwalar 'yan sanda
Sir Mike Mbama Okiro, tsohon sufeta janar na rundunar 'yan sandan Najeriya. Hoto: @david_azuh
Source: Twitter

Bukar hadin kan hukumomi

Okiro ya kuma soki yadda hukumomin tsaro ke tafiyar hawainiya wajen musayar bayanan sirri.

Ya ce lokacin yana Sufeto Janar ya taba rubuta wa Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro cewa jami’an tsaro su riƙa musayar bayanai kai tsaye maimakon jiran amincewa daga hedikwata.

Ya ce irin wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen dakile hare-haren masu aikata laifuka cikin gaggawa da kuma inganta tsaron ƙasa.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: An gano hanyar da aka kafa ma'aikatar bogi ta PFIPC

Dalilin karfin Boko Haram a Najeriya

Tun da fari, mun ruwaito cewa, tsohon IGP Mike Okiro ya ce rushe rundunar ATS da ya kafa ne ya ba Boko Haram damar samun ƙarfi da bazuwa a Najeriya.

Mike Okiro ya bayyana cewa ya horas da jami'an ATS a ƙasashen waje tare da kafa cibiyar horaswa a Ribas domin yaƙi da ta'addanci.

Tsohon sufeta janar din ya yi zargin cewa rashin goyon bayan gwamnati da dakatar da shirin ne ya raunana matakan dakile Boko Haram tun daga farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com