Bayanai Sun Fito: An Gano dalilin Tinubu na Yi wa Ribadu 'Kishiya' a Harkar Tsaro
- Bayanai na ci gaba da fitowa game da matakin Bola Tinubu na nadin sabon mai ba shi shawara kan tsaron cikin gida a Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa nadin na da alaka da rashin jituwar jami’an tsaro da mai ba shugaban kasa shawara, Nuhu Ribadu
- Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa sabon nadin zai taimaka wajen karfafa hadin gwiwar hukumomin tsaro da kawo sabuwar hanya wajen magance matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa nadin sabon mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaron cikin gida ya samo asali ne daga matsin lamba na jami’an tsaro.
Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun ce shugabannin sojoji da jami’an leken asiri sun nuna rashin jin dadinsu da yadda NSA, Nuhu Ribadu ke gudanar da aiki.

Source: Twitter
Dalilin nada Famadewa a ofishin tsaron cikin gida
Wata majiya ta fadawa Punch cewa shugabannin tsaro sun zargi Ribadu da shiga harkokin gudanar da ayyukan soja maimakon takaitawa wajen bai wa shugaban kasa shawara.
Majiyar ta bayyana cewa an fara ganin wani sabon tsari inda ake amfani da tawagar Nuhu Ribadu wajen gudanar da wasu ayyukan tsaro a fili.
A ranar 11 ga Mayu, 2026 shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Manjo Janar Adeyinka Fadewa mai ritaya a matsayin mai ba shi shawara.
Sanarwar da gwamnatin tarayya ta fitar ta ce nadin Fadewa zai taimaka wajen karfafa hadin gwiwar hukumomin tsaro da inganta tattara bayanan sirri.
Rahotanni sun ce shugaban kasa yana neman sabuwar hanya domin samun cikakken bayani kan matsalar tsaro da kuma kawo karshen rikicin shekaru masu yawa.
Wata majiya ta bayyana cewa gwamnati na kashe makudan kudade wajen yaki da matsalar tsaro maimakon amfani da kudin wajen inganta ilimi da hanyoyi.

Source: Twitter
Manufar nadin Famadewa domin taimakawa tsaro
Fadar shugaban kasa ta ce sabon mai bai wa shugaban kasa shawara da NSA Ribadu za su yi aiki tare domin samar da ingantaccen tsaro ga ’yan Najeriya.
Shugaba Tinubu ya buƙaci Janar Famadewa da ya yi amfani da dukkan kwarewarsa da kishin ƙasa wajen ganin an cimma muradun tsaron Najeriya.
Manufar wannan naɗi ita ce tabbatar da cewa hukumomin tsaro sun haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen gano barazana tun kafin ta auku ta hanyar amfani da fasahar zamani da leken asiri.
Wannan mataki dai na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar ƙalubale daban-daban na tsaro wanda ke jawo matsaloli a kasar, cewar Leadership.
Ribadu ya gana da mataimakin Trump a Amurka
Mun ba ku labarin cewa mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya tattauna batun yaki da ta'addanci tare da mataimakin shugaban Amurka.
Gwamnatocin Najeriya da Amurka sun ƙarfafa haɗin gwiwa wajen musayar bayanan sirri da kuma haɗin kan soja domin yaƙar Boko Haram da sauransu.
Shugaba kasa Bola Tinubu ya nuna godiya bisa ci gaba da tallafin horaswa da bayanan sirri da gwamnatin Amurka ke bai wa jami’an tsaron Najeriya.
Asali: Legit.ng


