'Yan Majalisar Wakilai na APC da Suka Sha Kaye a Zaben Fitar da Gwani

'Yan Majalisar Wakilai na APC da Suka Sha Kaye a Zaben Fitar da Gwani

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta gudanar da zaben fitar da gwani domin zabar 'yan takarar da za su nemi kujerun majalisar wakilai a zaben 2027
  • Wasu daga cikin 'yan majalisar da ke kan kujera sun shiga cikin zaben domin neman damar sake wakiltar mazabunsu
  • Sai dai, daga cikin 'yan majalisun da ke kan kujera, wasu sun fadi inda suka gaza samun tikitin sake tsayawa takara a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - 'Yan Majalisar wakilai da dama da ke kan kujera a halin yanzu sun gaza samun tikitin takarar komawa kan kujerunsu a inuwar jam'iyyar APC.

'Yan majalisun sun sha kashi ne yayin zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Mayun 2026 gabannin babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Maidoki: Sanatan APC a Kebbi ya fice daga jam'iyyar ana dab da zaben fitar da gwani

Wasu 'yan majalisar wakilai sun rasa tikiti
'Yan majalisar wakilai a zaman majalisa Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce daga cikin fitattun ’yan majalisar da suka rasa tikitin har da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Julius Ihonvbere.

'Yan majalisar APC sun rasa tikiti

Julius Ihonvbere wanda yake yunkurin neman tazarar wa’adi na uku domin wakiltar Mazaɓar Tarayya ta Owan a jihar Edo ya sha kaye a zaben fitar da gwanin.

Ya rasa tikitin APC ne a hannun tsohon kwamishinan ma’adinai, Andrew Ijegbai, sakamakon tsarin karba-karba tsakanin Owan Gabas da Owan Yamma.

A jihar Edo dai, wani ɗan majalisa mai ci, Eseosa Iyawe, ya rasa tikitin APC na mazaɓar tarayya ta Oredo a hannun tsohon Kwamishinan Ilimi, Dr. Paddy Iyamu.

Eseosa Iyawe yana cikin ’yan majalisar da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar LP amma suka sauya sheka zuwa APC bayan wasu shekaru a Majalisar wakilai.

'Yan majalisa 4 sun rasa tikiti a Imo

A jihar Imo kuwa, an hana 'yan majalisa masu ci guda huɗu tikitin takarar komawa kan kujerunsu, jaridar The Nation ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Yusuf Buhari ya san matsayarsa bayan kammala zaben fitar da gwani na APC a Katsina

Sun haɗa da Matthew Nwogu mai wakiltar Aboh Mbaise/Ngor Okpala, Miriam Onuoha na Okigwe Kudu, Harrison Nwadike mai wakiltar Isu/Njaba/Nkwerre/Nwangele, da kuma Emeka Martins Chinedu na Mazaɓar Tarayya ta Ahiazu/Ezinihitte.

Haka kuma abin ya shafi Ismail Kayode, mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Ifelodun/Oyun/Offa a jihar Kwara, wanda ya sha kaye a hannun tsohon babban sakataren yaɗa labarai na Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, wato Rafiu Ajakaye.

A jihar Kebbi, ɗan majalisa mai ci Mansur Musa Jega ya rasa tikitin APC na mazaɓar tarayya ta Jega/Gwandu/Aleiro sakamakon wani tsari na maslaha wanda ya samar da tsohon shugaban Hukumar gidajen gyaran hali na Najeriya, Jafar Ahmed Jega.

Wasu 'yan majalisar APC sun rasa tikitin takara
'Yan majalisar wakilan Najeriya a zaman majalisa Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

'Yan majalisa sun rasa tikiti a Jigawa

Haka zalika, 'yan majalisa hudu masu ci a jihar Jigawa sun rasa tikitin komawa takararsu yayin zaɓen fitar da gwanin.

Su ne Muktar Muhammad mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Kazaure/Roni/Gwiwa/Yankwashi, Ibrahim Usman Auyo na mazaɓar tarayya ta Hadejia/Auyo/Kafin Hausa, Sa’adu Wada Taura mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Ringim/Taura, da kuma Yusuf Sa’idu Miga na mazaɓar tarayya ta Jahun/Miga.

Sanata Maidoki ya fice daga APC

Kara karanta wannan

Tinubu ya aika sako ga 'yan APC ana shirin fara zaben fitar da gwani

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta rasa daya daga cikin sanatocin da take da su a jihar Kebbi ta tarayyar Najeriya.

Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu, Garba Musa Maidoki, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Garba Musa Maidoki ya bayyana cewa ya fice daga jam'iyyar ne saboda rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng